Yabi Ubanmu, ya Raina
Ta Dawuda.
Jerin alherai na Ubanmu ne da ba za a manta da su ba — an gafarta zunubai, an warkar da cututtuka, an fanshi rai daga rami. A tsakiyarsa akwai kwatanci: kamar yadda zuciyar uba take kai wa ga 'ya'yansa, haka tasa take kai wa gare mu. Yana tunawa cewa mu ƙura ne.
103 1Yabi Ubanmu, ya raina; dukan abin da yake cikina kuma, yă yabi sunansa mai tsarki!
2Yabi Ubanmu, ya raina, kada kuma ka manta da ko ɗaya daga cikin alheransa, 3wanda yake gafarta dukan zunubanka, wanda yake warkar da dukan cututtukanka, 4wanda yake fansar ranka daga kabari, wanda yake naɗa maka rawanin madawwamiyar ƙauna da jinƙai, 5wanda yake ƙosar da kai da abubuwa masu kyau muddin kana da rai, don a sabunta ƙuruciyarka kamar ta gaggafa.
6Ubanmu yana aikata adalci da shari'a ta gaskiya domin dukan waɗanda ake zaluntarsu.
7Ya sanar wa Musa hanyoyinsa, ayyukansa kuwa ga mutanen Isra'ila. 8Ubanmu mai jinƙai ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan madawwamiyar ƙauna. 9Ba zai yi zargi kullum ba, ba kuma zai riƙe fushinsa har abada ba. 10Ba ya yi da mu bisa ga zunubanmu ba, ba ya kuma saka mana bisa ga laifofinmu ba. 11Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girman madawwamiyar ƙaunarsa yake ga masu tsoronsa; 12kamar yadda gabas take da nisa daga yamma, haka Ubanmu ya kawar da zunubanmu daga gare mu.
13Kamar yadda uba yake tausaya wa 'ya'yansa, haka Ubanmu yake tausaya wa masu tsoronsa. 14Gama ya san yadda aka halicce mu; ya tuna cewa mu ƙura ne. 15Kwanakin mutum kamar ciyawa suke; yana hudawa kamar furen jeji; 16gama iska ta wuce a kansa, sai ya ƙare, wurinsa kuma ba ya ƙara saninsa ba. 17Amma madawwamiyar ƙaunar Ubanmu tana nan daga madawwami har madawwami ga masu tsoronsa, adalcinsa kuma ya kai ga 'ya'yan 'ya'ya, 18ga waɗanda suke kiyaye alkawarinsa, suke kuma tunawa su aikata umarnansa.
19Ubanmu ya kafa gadon sarautarsa a sammai, mulkinsa kuma yana mulki a bisa dukan kome.
20Ku yabi Ubanmu, ku mala'ikunsa, ku jarumai masu ƙarfi masu aikata maganarsa, kuna biyayya ga kowace kalmarsa! 21Ku yabi Ubanmu, dukan rundunoninsa, bayinsa masu aikata nufinsa! 22Ku yabi Ubanmu, dukan ayyukansa, a ko'ina a cikin mulkinsa. Yabi Ubanmu, ya raina!