Kora Ya Tayar wa Musa
Kora da shugabanni 250 suka ce dukan jama'a tsarkaka ne, saboda haka ba wanda yake bukatar a kawo shi kusa a madadinsu. Musa ya bar faranti na ƙona turare su yanke hukunci. Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan da Abiram, wuta ta cinye mutum 250ɗin, Ubanmu kuma da kansa ya amsa wannan da'awa.
16 1Kora ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ya tara mutane, tare da Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab, da On ɗan Felet, 'ya'yan Ra'ubenu. 2Suka tsaya a gaban Musa tare da shugabannin jama'ar Isra'ila mutum 250—zaɓaɓɓun mutanen taro, fitattun mutane. 3Suka taru gāba da Musa da Haruna suka ce, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama'a masu tsarki ne, dukansu, Ubanmu kuwa yana cikinsu. Don me kuke ɗaukaka kanku bisa taron Ubanmu?”
4Da Musa ya ji haka, sai ya fāɗi rubda ciki. 5Ya ce wa Kora da dukan jama'arsa, “Da safe, Ubanmu zai nuna wa ne nasa, da kuma wa ke mai tsarki, zai kuma kawo shi kusa da kansa. Wanda ya zaɓa, shi zai kawo kusa da kansa. 6Ku yi haka: ku ɗauki farantan turare, kai Kora da dukan jama'arka. 7Gobe ku sa wuta a cikinsu, ku zuba turare a kansu a gaban Ubanmu. Mutumin da Ubanmu ya zaɓa, shi ne zai zama mai tsarki. Kun wuce gona da iri, ku 'ya'yan Lawi!”
8Musa kuma ya ce wa Kora, “Ku saurara yanzu, ku 'ya'yan Lawi: 9Bai isar muku ba ne cewa Uban Isra'ila ya keɓe ku daga sauran jama'ar Isra'ila, don yă kawo ku kusa da kansa, don ku yi aikin tabanakul na Ubanmu, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu hidima? 10Ya kawo ku kusa—kai da dukan 'yan'uwanka, 'ya'yan Lawi—duk da haka yanzu kuna neman firistanci ma? 11Kai da dukan ƙungiyarka kun taru gāba da Ubanmu. Haruna kuwa—me ne shi, da kuke gunaguni gāba da shi?”
12Musa ya aika a kirawo Datan da Abiram, 'ya'yan Eliyab. Suka ce, “Ba za mu zo ba! 13Bai isa ba ne cewa ka fito da mu daga ƙasa mai zub da madara da zuma don ka kashe mu a jeji, har kana so ka yi mulki a kanmu kuma? 14Ban da haka, ba ka kawo mu ƙasa mai zub da madara da zuma ba, ba ka kuwa ba mu gonaki da gonakin inabi gādo ba. Za ka ƙwaƙule idanun mutanen nan ne? Ba za mu zo ba!”
15Musa ya husata ƙwarai ya ce wa Ubanmu, “Kada ka kula da hadayarsu. Ban ƙwace ko jaki ɗaya daga gare su ba, ban kuma yi wa ko ɗayansu laifi ba.”
16Musa ya ce wa Kora, “Kai da dukan jama'arka, ku gabatar da kanku a gaban Ubanmu gobe—kai, da su, da Haruna. 17Kowane mutum yă ɗauki farantin turarensa, yă zuba turare a kansa, yă kawo shi a gaban Ubanmu—farantan turare 250—kai da Haruna, kowanne da farantinsa.”
18Kowanne ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta a cikinsa ya kuma zuba turare a kansa, suka tsaya tare da Musa da Haruna a ƙofar alfarwar sujada. 19Kora ya tara dukan jama'a gāba da su a ƙofar alfarwar sujada; sai ɗaukakar Ubanmu ta bayyana ga dukan jama'a.
20Sai Ubanmu ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce,
21“Ku ware kanku daga wannan jama'a, domin in hallaka su nan take.”
22Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki suka yi kuka suka ce, “Ya Ubanmu, Uban ruhohin dukan 'yan adam—in mutum ɗaya ya yi zunubi, za ka yi fushi da dukan jama'a ne?” 23Sai Ubanmu ya ce wa Musa,
24“Ka gaya wa jama'a, su rabu daga wuraren zaman Kora, da Datan, da Abiram.”
25Sai Musa ya tashi ya tafi wurin Datan da Abiram, dattawan Isra'ila kuwa suka bi shi. 26Ya ce wa jama'a, “Ku rabu da tentunan mugayen mutanen nan. Kada ku taɓa kome nasu, don kada a kawar da ku cikin dukan zunubansu.”
27Sai suka janye daga tentunan Kora, da Datan, da Abiram ta kowane gefe, Datan da Abiram kuwa suka fito suka tsaya a ƙofofin tentunansu tare da matansu, da 'ya'yansu, da ƙananan yaransu.
28Musa ya ce, “Ga yadda za ku san Ubanmu ne ya aiko ni in yi dukan waɗannan abubuwa, kuma cewa babu ko ɗaya daga cikinsu da ya fito daga ra'ayina: 29In mutanen nan suka mutu mutuwa irin ta kowa, suka sami makomar kowane mutum, to, ba Ubanmu ne ya aiko ni ba. 30Amma in Ubanmu ya yi wani sabon abu, ƙasa kuwa ta buɗe bakinta ta haɗiye su tare da dukan abin da yake nasu, suka kuma gangara da rai zuwa kabari, to, za ku san mutanen nan sun rena Ubanmu.”
31Nan da nan da ya gama faɗin dukan wannan, sai ƙasa ta tsage a ƙarƙashinsu, 32ƙasa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su, da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan dukiyarsu. 33Su da dukan abin da yake nasu suka gangara da rai zuwa kabari; ƙasa ta rufe a kansu, aka kuwa hallaka su daga cikin taro. 34Dukan Isra'ilan da suke kewaye da su suka gudu saboda kukansu, gama suka ce, “Ƙasa za ta iya haɗiye mu ma!” 35Sai wuta ta fito daga wurin Ubanmu ta cinye mutum 250 da suke miƙa turaren.