Hannun Uba cikin Auren Samson
Samson ya nace sai ya auri Bafilistiya duk da ƙin iyayensa, ba tare da sanin cewa Ubanmu yana shirya wata dama a kan masu mulkin Isra'ila ba. Ya kashe zaki da hannu, ya ci zuma daga gawarsa, ya mai da shi kacici-kacici. Hawayen matarsa suka fitar da amsar, mutum talatin kuma suka mutu saboda haka.
14 1Samson ya gangara zuwa Timna, a can kuwa ya ga wata budurwa, ɗaya daga cikin 'ya'yan matan Filistiyawa. 2Ya hau ya gaya wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya ce, “Na ga wata mace Bafilistiniya a Timna; yanzu sai ku nemo mini ita tă zama matata.”
3Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce masa, “Babu wata mace a cikin 'yan'uwanka ko cikin dukan mutanena, har da za ka auro mata daga Filistiyawa marasa kaciya?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ka nemo mini ita, domin ita ce ta yi mini daidai a idanuna.”
4Mahaifinsa da mahaifiyarsa ba su san cewa wannan daga Ubanmu ne ba, wanda yake neman dalili yă yi gāba da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa suke mulkin Isra'ila.
5Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Da suka isa gonakin inabi na Timna, sai wani ɗan zaki ya zo masa da ruri. 6Sai Ruhun Ubanmu ya sauko masa da ƙarfi, ya kuma yayyage zakin da hannuwansa kawai kamar ɗan akuya, amma bai gaya wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa abin da ya yi ba. 7Sa'an nan ya gangara ya yi magana da macen, ita kuwa ta yi daidai a idanun Samson.
8Bayan wani lokaci, da yake komowa don yă aure ta, sai ya ratse don yă dubi mushen zakin. Sai ga tarin ƙudan zuma a cikinsa, da kuma zuma. 9Ya kwankwaɗo zuman a hannuwansa, yana ci yana tafiya. Da ya isa wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya ba su, su kuwa suka ci. Amma bai gaya musu cewa daga mushen zaki ya kwankwaɗo ta ba. 10Mahaifinsa ya gangara wurin macen, Samson kuwa ya yi biki a can, yadda samari suke yi. 11Da mutanen suka gan shi, sai suka kawo abokai talatin su kasance tare da shi.
12Samson ya ce musu, “Bari in ba ku wata kacici-kacici. In kuka warware ta cikin kwanaki bakwai na bikin, zan ba ku mayafan lilin talatin da kaya talatin na sauyawa. 13Amma in kuka kāsa amsawa, sai ku ba ni mayafan lilin talatin da kaya talatin na sauyawa.” Suka ce, “Faɗi kacici-kacicinka, mu ji.”
14Ya ce, “Daga mai ci abin ci ya fito; daga mai ƙarfi abu mai zaƙi ya fito.” Kwana uku ba su iya warware kacici-kacicin ba.
15A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki yă bayyana mana kacici-kacicin, in ba haka ba za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Ko kin gayyace mu nan ne domin a washe mu?”
16Matar Samson ta yi kuka a kansa, tana cewa, “Kana ƙina kawai, ba ka ƙaunata ba. Ka ba mutanena kacici-kacici amma ba ka gaya mini amsarsa ba.” Ya ce, “Ban gaya wa mahaifina ko mahaifiyata ba, to yaya zan gaya miki?”
17Ta yi ta kuka a kansa cikin kwanaki bakwai na bikinsu, a rana ta bakwai kuwa ya gaya mata, domin ta matsa masa. Sai ta gaya wa mutanenta kacici-kacicin. 18A rana ta bakwai, kafin fāɗuwar rana, mutanen garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaƙi? Me ya fi zaki ƙarfi?” Samson ya amsa ya ce, “Da ba ku yi noma da karsanata ba, da ba ku warware kacici-kacicina ba.”
19Sai Ruhun Ubanmu ya sauko masa da ƙarfi. Ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutane talatin daga cikinsu, ya kwashe kayansu, ya kuma ba da tufafinsu ga waɗanda suka warware kacici-kacicin. Yana cike da fushi, sai ya hau zuwa gidan mahaifinsa. 20Aka ba da matar Samson ga abokinsa, wanda ya kasance abokin angonsa.