Kuringar Inabi da Mai Lambu
Shi ne kurangar inabi, Ubansa ne manomi, kuma 'ya'ya suna fitowa ne kawai ta wurin kasancewa a haɗe da shi. Ya kira su abokai maimakon bayi, ya kuma gaya musu duk abin da ya ji daga wurin Ubansa. Sa'an nan gargaɗin: duniyar da ta ƙi shi za ta ƙi su su ma.
15 1“Ni ne kuringar inabi ta gaskiya, Ubana kuwa shi ne mai lambu. 2Kowane reshe a cikina wanda ba ya ba da 'ya'ya, yakan cire shi; kuma kowane reshe mai ba da 'ya'ya, yakan datse shi, domin yă ƙara ba da 'ya'ya. 3Ku kam, kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na gaya muku. 4Ku zauna a cikina, ni kuma in zauna a cikinku. Kamar yadda reshe ba ya iya ba da 'ya'ya shi kaɗai, sai dai ya zauna a cikin kuringar inabin, haka ku ma ba za ku iya ba sai kun zauna a cikina. 5Ni ne kuringar inabin, ku ne rassan. Duk wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, yana ba da 'ya'ya da yawa, gama in ban da ni ba za ku iya yin kome ba. 6Duk wanda bai zauna a cikina ba, akan jefar da shi waje kamar reshe, yă kuma bushe; akan tara rassan, a jefa su cikin wuta, su ƙone. 7Idan kuka zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku shi. 8Ta haka ake ɗaukaka Ubana, wato ku ba da 'ya'ya da yawa, ku kuma zama almajiraina.
9“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. Ku zauna cikin ƙaunata. 10Idan kuka kiyaye umarnaina, za ku zauna cikin ƙaunata, kamar yadda na kiyaye umarnan Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunarsa. 11Na faɗa muku wannan ne domin farin cikina yă kasance a cikinku, farin cikinku kuma yă zama cikakke.
12“Ga umarnina, ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Babu wanda yake da ƙauna mafi girma fiye da wannan, wato mutum yă ba da ransa saboda abokansa. 14Ku abokaina ne idan kun yi abin da na umarce ku. 15Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, domin bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. Na ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. a a v15 Yesu yana mai da almajirai daga bauta zuwa abuta ta wurin bayyana musu duk abin da ya ji daga wurin Ubansa — wannan shi ne nufin zuciyar Uba ga kowane mai karatu, wato abuta ta wurin Ɗa. 16Ba ku ne kuka zaɓe ni ba — ni ne na zaɓe ku, na kuma naɗa ku domin ku tafi ku ba da 'ya'ya masu dawwama, domin duk abin da kuka roƙi Uba da sunana, yă ba ku. 17Ga umarnina gare ku, ku ƙaunaci juna.
Sa'ad da Duniya Ta Ƙi Ku
18“Idan duniya ta ƙi ku, ku sani ta ƙi ni kafin ku. 19Da ku na duniya ne, da duniya ta ƙaunace ku a matsayin nata. Amma ku ba na duniya ba ne; a maimakon haka, na zaɓe ku daga cikin duniya, shi ya sa duniya take ƙin ku. 20Ku tuna da abin da na gaya muku, wato bawa ba ya fi maigidansa girma ba. In sun tsananta mini, za su tsananta muku ku ma; in sun kiyaye maganata, za su kiyaye taku ma. 21Amma za su yi muku wannan duka saboda sunana, domin ba su san wanda ya aiko ni ba. 22Da ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi; amma yanzu ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23Duk wanda ya ƙi ni, ya ƙi Ubana ne ma. 24Da ban yi ayyukan da babu wani ya taɓa yi a cikinsu ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi ni da Ubana duka. 25Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Shari'arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’
26“Sa'ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba — Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba — shi zai ba da shaida a kaina. b b v26 Mai Taimako da Yesu ya yi alkawari shi ne Ruhu Mai Tsarki — wanda Yesu yake aikowa daga wurin Uba, wanda aka kira a nan “Ruhun gaskiya” domin yana bi da almajirai cikin dukan abin da Yesu ya bayyana.
27“Ku ma dole ne ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun farko.”