Ubanmu Ya Yi Magana
Ubanmu da kansa ya faɗi kalmomin nan goma, ya fara ba da umarni ba, amma da wanda yake: shi ne wanda ya fito da su daga bauta. Aminci, suna, Asabar, iyaye, rai, aure, dukiya, gaskiya, sha'awa. Jama'a suka roƙi Musa ya saurara a madadinsu, shi kuma ya shiga duhu ƙirin.
20 1Sa'an nan Ubanmu ya furta dukan waɗannan kalmomi, ya ce,
2“Ni ne Ubanka, wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.
3“Kada ka kasance da waɗansu alloli dabam a gabana.
4“Kada ka yi wa kanka siffa sassaƙaƙƙiya, ko kamannin kome da yake a bisa a sammai, ko a ƙasa a duniya, ko a cikin ruwa da yake ƙarƙashin ƙasa. 5Kada ka rusuna musu, kada kuma ka bauta musu; Ni Ubanka, Uba ne mai kishi, mai saukar da zunubin iyaye a kan 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na masu ƙina, 6amma ina nuna madawwamiyar ƙauna ga dubban mutane masu ƙaunata da suke kiyaye umarnaina.
7“Kada ka ambaci sunan Ubanka a banza, gama Ubanmu ba zai kuɓutar da wanda ya ambaci sunansa a banza ba.
8“Ka tuna da ranar Asabar, ka kiyaye ta da tsarki. 9Kwana shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan ayyukanka, 10amma rana ta bakwai Asabar ce ga Ubanka. Kada ka yi wani aiki a cikinta—kai, ko ɗanka, ko 'yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko dabbobinka, ko baƙon da yake cikin ƙofofinka. 11Gama cikin kwana shida Ubanmu ya yi sammai, da ƙasa, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, sa'an nan ya huta a rana ta bakwai; saboda haka Ubanmu ya albarkaci ranar Asabar, ya kuma tsarkake ta.
12“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin kwanakinka su yi tsawo a ƙasar da Ubanka yake ba ka.
13“Kada ka yi kisankai.
14“Kada ka yi zina.
15“Kada ka yi sata.
16“Kada ka yi shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.
17“Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko bawansa, ko baiwarsa, ko bijiminsa, ko jakinsa, ko wani abu da yake na maƙwabcinka.”
18Dukan mutane suka ga tsawa, da walƙiya, da karar ƙaho, da dutsen yana hayaƙi. Da suka ga haka, sai suka yi rawar jiki, suka tsaya daga nesa.
19Suka ce wa Musa, “Kai ka yi mana magana, mu kuwa za mu saurara. Amma kada Ubanmu ya yi magana da mu, don kada mu mutu.”
20Musa ya ce wa mutanen, “Kada ku ji tsoro; Ubanmu ya zo ne domin yă gwada ku, domin tsoronsa yă kasance tare da ku, don kada ku yi zunubi.” 21Mutanen suka tsaya daga nesa, Musa kuwa ya matso kusa da baƙin duhun nan inda Ubanmu yake.
Musa Ya Matso Kusa
22Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka gaya wa Isra'ilawa cewa, ku da kanku kun ga yadda na yi magana da ku daga Sama. 23Kada ku yi wa kanku allolin azurfa gefe da ni, kada kuma ku yi wa kanku allolin zinariya. 24Ku yi mini bagade na ƙasa, a kansa kuma ku miƙa hadayunku na ƙonawa da hadayunku na salama, tumakinku da shanunku. Duk inda na sa a tuna da sunana, zan zo wurinku in albarkace ku. 25In kuka yi mini bagade na dutse, kada ku gina shi da duwatsun da aka sassaƙa, gama idan kun yi amfani da kayan aikinku a kansa, kun ƙazantar da shi. 26Kada ku hau matakai zuwa bagadena, don kada tsiraicinku yă bayyana a kansa.”