Gaisuwa ga Tasalonikawa
Wasiƙa ta biyu da take kafa ikilisiyar da ta ruɗe game da ranar Ubangiji, tana kuma kiransu su tsaya daram.
1 1Bulus, da Silbanus, da Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Tasalonikawa wadda take cikin Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu: 2Alheri gare ku da salama daga wurin Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
Godiya saboda Karuwar Bangaskiyarku
3Ya kamata mu dinga godiya ga Ubanmu kullum saboda ku, 'yan'uwa—daidai ne haka—domin bangaskiyarku tana ƙaruwa ƙaruwa, kuma kowannenku yana ƙaruwa cikin ƙauna ga juna. 4Saboda haka mu kanmu muna taƙama da ku a cikin ikkilisiyoyin Ubanmu, saboda jimrinku da bangaskiyarku a cikin dukan tsanani da wahalhalun da kuke sha.
5Wannan shaida ce ta shari'ar Ubanmu mai adalci, cewa an lissafta ku a matsayin masu-cancanta ga Mulkin Ubanmu, wanda saboda shi kuke shan wahala. 6Tun da Ubanmu mai adalci ne, zai sāka wa waɗanda suke ba ku wahala da wahala, 7yă kuma ba ku hutu, ku da kuke shan wahala, tare da mu, sa'ad da za a bayyana Ubangiji Yesu daga Sama tare da mala'ikunsa masu-iko, 8cikin harshen wuta, yana hukunta waɗanda ba su san Ubanmu ba, da kuma waɗanda ba su yi biyayya ga bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9Za su sha hukuncin hallaka madawwamiya, a rabe daga gaban Ubangiji da ikonsa mai ɗaukaka, 10a ranan nan, sa'ad da ya zo domin a ɗaukaka shi cikin tsarkakansa, a kuma yi mamakinsa a cikin dukan waɗanda suka gaskata—domin an gaskata shaidarmu gare ku.
11Saboda wannan muke yin addu'a dominku kullum, domin Ubanmu yă lissafta ku a matsayin masu-cancantar kiransa, yă kuma cika ta wurin ikonsa kowace sha'awar nagarta da kowane aikin bangaskiya, 12domin a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, ta wurin alherin Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.