Ranar Ubangiji Tana Zuwa
Ranar tana zuwa kamar ɓarawo, amma su ba a cikin duhu suke game da ita ba, saboda haka su zauna a faɗake da natsuwar hankali. Ƙarshen jeri ne mai sauri: ku girmama shugabanninku, ku ƙarfafa masu karaya, ku yi haƙuri, ku yi farin ciki, ku yi addu'a, ku yi godiya, ku gwada kome, ku riƙe abin da yake nagari.
5 1Game da lokuta da zamanu kuwa, 'yan'uwa, ba kwa bukatar a rubuta muku kome. 2Ku kanku kun sani sarai cewa ranar Ubangijinmu Yesu za ta zo kamar barawo da dare. 3Sa'ad da mutane suke cewa, “Salama da zaman lafiya,” sai halaka ta auko musu farat ɗaya—kamar naƙudar haihuwa ga mace mai ciki—ba kuwa za su tsere ba. 4Amma ku, 'yan'uwa, ba kwa cikin duhu da zai sa ranar nan ta auko muku da mamaki kamar barawo. 5Dukanku 'ya'yan haske ne da 'ya'yan rana; mu ba na dare ba ne, ba kuwa na duhu ba. 6Saboda haka, kada mu yi barci kamar sauran mutane, sai dai mu zauna a faɗake, muna kuma a natse. 7Gama masu barci da dare suke barci, masu buguwa kuma da dare suke buguwa. 8Amma tun da mu na rana ne, bari mu kasance a natse, muna sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen ceto kuma kamar hula ta ƙarfe. 9Gama Ubanmu bai ƙaddara mu ga fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, 10wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a faɗake ko muna barci, mu rayu tare da shi. 11Saboda haka ku ƙarfafa juna, ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi.
Rayuwa a Matsayin 'Ya'yan Haske
12Muna roƙonku, 'yan'uwa, ku girmama waɗanda suke aiki tuƙuru a cikinku, suke bi da ku cikin Ubangiji, suke kuma gyara ku. 13Ku ƙwarai da gaske ku ɗauke su da daraja cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku zauna lafiya da juna.
14'Yan'uwa, muna gargaɗinku, ku gyara masu ƙyuya, ku ta'azantar da waɗanda suka karaya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa. 15Ku lura kada kowa yă rama mugunta da mugunta ga kowa, sai dai kullum ku nemi alheri ga juna da kuma ga kowa.
16Ku yi farin ciki kullum, 17ku yi addu'a babu fasawa, 18ku yi godiya cikin kome; gama wannan shi ne nufin Ubanmu dominku cikin Almasihu Yesu. 19Kada ku kashe Ruhu Mai Tsarki. 20Kada ku rena annabce-annabce, 21sai dai ku gwada kome; ku riƙe abin da yake nagari. 22Ku nisanci kowace irin mugunta.
23Bari Ubanmu na salama kansa yă tsarkake ku ɗungum, bari kuma a kiyaye ruhunku da ranku da jikinku duka marar aibi a zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu. 24Mai kiranku mai aminci ne; lalle zai kuwa cika shi.
25'Yan'uwa, ku yi mana addu'a.
26Ku gai da dukan 'yan'uwa da sumba mai tsarki. 27Ina dokarku a gaban Ubangiji a karanta wannan wasiƙa ga dukan 'yan'uwa.
28Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă kasance tare da ku.