Tafiya a Hanyar da take Faranta wa Ubanmu Rai
Da farko tsarki a aikace: tsabtar jima'i, rashin cuta wa ɗan'uwa, kula da harkar kanka, da aiki da hannunka don kada ka dogara ga kowa. Sa'an nan amsar baƙin cikinsu: ba za a bar matattu a baya ba, amma Ubanmu zai kawo su gida da farko sa'ad da Ubangiji ya zo.
4 1A ƙarshe dai, 'yan'uwa, muna roƙonku muna kuma gargaɗinku cikin Ubangiji Yesu cewa, kamar yadda kuka karɓa daga gare mu yadda ya kamata ku yi tafiyarku ku kuma faranta wa Ubanmu rai—kamar yadda kuke yi kuwa—ku ƙara yin haka. 2Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin Ubangiji Yesu. 3Gama wannan shi ne nufin Ubanmu: tsarkakewarku—wato ku nisanci fasikanci, 4kowannenku kuma yă san yadda zai auri mata cikin tsarki da daraja, 5ba cikin sha'awar kwaɗayi kamar al'umman da ba su san Ubanmu ba, 6kada kuma wani yă yi wa ɗan'uwansa laifi ko yă cuce shi a wannan al'amari, domin Ubangiji mai ɗaukar fansa ne cikin dukan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka faɗa muku a dā muka kuma yi muku kashedi sosai. 7Gama Ubanmu bai kira mu ga ƙazanta ba, sai dai cikin tsarki. 8Saboda haka duk wanda ya ƙi wannan, ba mutum ya ƙi ba ne, sai dai Ubanmu, wanda yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki. a a v8 A nan Ubanmu yana ba da Ruhunsa Mai Tsarki — an ambaci Uba da Ruhu tare, suna jawo mai karatu cikin ƙaunar da take tsarkake mu.
9Game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ba kwa bukatar wani yă rubuta muku, gama ku da kanku Ubanmu ne ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10Hakika kuwa kuna yin haka ga dukan 'yan'uwa ko'ina a Makidoniya. Amma muna gargaɗinku, 'yan'uwa, ku ƙara yin haka, 11ku kuma mai da niyyarku ku yi zaman natsuwa, ku kula da sha'anoninku, ku kuma yi aiki da hannuwanku, kamar yadda muka umarce ku, 12domin ku yi tafiya yadda ya dace a gaban waɗanda suke waje, kada kuma ku dogara ga kowa.
Uba Yana Dawo da 'Ya'yansa Gida
13Ba ma so ku kasance cikin jahilci, 'yan'uwa, game da waɗanda suka yi barci, domin kada ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14Gama tun da muka gaskata cewa Yesu ya mutu ya kuma tashi, haka ma Ubanmu zai kawo tare da shi, ta wurin Yesu, waɗanda suka yi barci. 15Gama wannan muke gaya muku ta wurin maganar Ubangiji: mu da muke da rai, muka kuma ragu har zuwa dawowar Ubangiji, lalle ba za mu riga waɗanda suka yi barci ba. 16Gama Ubangiji da kansa zai sauko daga Sama da kirar umarni, da muryar babban mala'ika, da kuma ƙahon Ubanmu, matattu kuwa cikin Almasihu za su fara tashi. 17Sa'an nan, mu da muke da rai har yanzu muka kuma ragu, za a ɗauke mu tare da su zuwa cikin gizagizai, mu taryi Ubangiji a sararin sama; ta haka kuwa za mu kasance tare da Ubangiji kullum. 18Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.