Hanun Ya Wulaƙanta Barorin Dawuda
Dawuda ya aika da ta'aziyya ga sabon sarkin Ammon, wanda mashawartansa suka rinjaye shi cewa jakadun 'yan leƙen asiri ne. Aka aske rabin gemunsu aka yanke rigunansu har kugu. Ammon ya yi hayar rundunonin Aram; Yowab ya raba sojojinsa da Abishai, sa'an nan ya bar sakamakon ga Ubanmu.
10 1Bayan haka, sai sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa Hanun ya gāje shi a matsayin sarki. 2Dawuda ya ce, “Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahash, kamar yadda mahaifinsa ya nuna mini alheri.” Saboda haka ya aiki barori su yi masa ta'aziyya saboda mutuwar mahaifinsa. Amma sa'ad da barorin Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa, 3sai shugabannin Ammonawa suka ce wa Hanun ubangijinsu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko maka mutane su yi maka ta'aziyya? Ashe, ba domin yă bincika birnin, yă leƙo asirinsa, yă kuma rushe shi ne Dawuda ya aiko maka barorinsa ba?”
4Sai Hanun ya kama barorin Dawuda, ya aske rabin gemun kowannensu, ya yanke tufafinsu har ƙugu, sa'an nan ya sallame su. 5Da aka gaya wa Dawuda, sai ya aiki manzanni su tarye su, domin mutanen sun ji kunya ƙwarai. Sarkin ya ce, “Ku zauna a Yariko sai gemunku ya sāke tsirowa, sa'an nan ku dawo.”
6Da Ammonawa suka ga sun zama abin ƙyama ga Dawuda, sai suka aika suka ɗauki Arameyawan Bet-rehob da Arameyawan Zoba haya—sojoji ƙasa dubu ashirin—da sarkin Ma'aka tare da mutum dubu ɗaya, da mutanen Tob dubu goma sha biyu. 7Da Dawuda ya ji haka, sai ya aiki Yowab tare da dukan rundunar jarumawa. 8Sai Ammonawa suka fito suka ja dāgā a bakin ƙofar birni, Arameyawan Zoba da na Rehob da mutanen Tob da na Ma'aka kuma suka tsaya dabam a fili.
9Da Yowab ya ga an fuskance shi da dāgā a gaba da kuma a baya, sai ya zaɓi waɗansu zaɓaɓɓun jarumawan Isra'ila, ya ja dāgā gāba da Arameyawa. 10Saurun kuma ya danƙa a hannun ɗan'uwansa Abishai, domin su ja dāgā gāba da Ammonawa. 11Yowab ya ce, “In Aram ya fi ƙarfina, sai ka zo ka cece ni; in kuwa Ammonawa suka fi ƙarfinka, ni kuma zan zo in cece ka. 12Ka ƙarfafa, mu yi ƙarfin hali saboda mutanenmu da kuma biranen Ubanmu. Bari Ubanmu yă yi abin da ya ga ya fi kyau a gare shi.” 13Sa'an nan Yowab da sojojin da suke tare da shi suka nufi Arameyawa don su yi yaƙi, sai suka gudu a gabansa. 14Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, su ma sai suka gudu a gaban Abishai, suka shiga birni. Sai Yowab ya janye daga Ammonawa ya koma Urushalima.
15Da Arameyawa suka ga Isra'ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke taruwa wuri ɗaya. 16Hadadezer ya aika aka kirawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yufretis; suka zo Helam, Shobak shugaban rundunar Hadadezer kuwa yana shugabantansu. 17Da Dawuda ya ji haka, sai ya tara dukan Isra'ila, ya haye Urdun, ya isa Helam. Arameyawa suka ja dāgā gāba da Dawuda suka yi yaƙi da shi. 18Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra'ila. Dawuda ya kashe mahayan kekunan yaƙinsu ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba'in, sa'an nan ya karkashe Shobak shugaban rundunarsu, wanda ya mutu a nan. 19Da dukan sarakunan da suke ƙarƙashin Hadadezer suka ga Isra'ila ta ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra'ila suka kuma bauta musu. Saboda haka Arameyawa suka ji tsoron sāke taimakon Ammonawa.