Mai Bayarwa da Farin Ciki
Bulus ya riga ya yi wa Makidoniya fahariya cewa Akaya a shirye take, don haka ya aiki mutane su riga shi. Yana so a ba da kyautar da yardar rai, ba da tilas ba, domin Ubanmu yana ƙaunar mai bayarwa da daɗin rai, kuma domin kuɗin zai zama godiya a tsakanin mutanen da Korantiyawa ba za su taɓa gani ba.
9 1Game da yi wa mutanen Ubangiji hidima, ba na bukatar in rubuta muku, 2gama na san marmarinku, ina kuma taƙama da ku a gaban mutanen Makidoniya, cewa Akaya ta shirya tun bara, himmarku kuma ta zuga yawancinsu. 3Saboda haka ina aika 'yan'uwan, domin taƙaman da muka yi game da ku kada ta zama a banza a wannan batu—domin ku kasance a shirye, yadda na faɗa. 4In ba haka ba, idan mutanen Makidoniya suka zo tare da ni suka same ku ba a shirye ba, mu—balle ku—za mu sha kunya saboda irin wannan tabbaci. 5Saboda haka na ga ya dace in gargaɗi 'yan'uwan su riga ku zuwa gare ku, su kuma shirya tun da wuri kyautar alheri da kuka yi alkawari, domin ta kasance a shirye kamar kyauta ta yardar rai, ba kamar wani abu da aka bayar da rashin yarda ba.
6Ku tuna da wannan: duk wanda ya shuka kaɗan, kaɗan zai girba, duk kuma wanda ya shuka da yawa, da yawa zai girba. 7Kowa yă bayar yadda ya yanke shawara a zuciyarsa, ba da ɓacin rai ba, ba kuma da tilas ba, gama Ubanmu yana ƙaunar mai bayarwa da farin ciki. 8Ubanmu yana da ikon sa kowane irin alheri yă yalwata gare ku, domin kullum kuna da duk abin da kuke bukata cikin kome, ku yalwata cikin kowane kyakkyawan aiki. 9Kamar yadda yake a rubuce: “Ya watsa kyautansa ga matalauta; adalcinsa yana dawwama har abada.”
10Shi wanda yake ba da iri ga mai shuka da kuma abinci don ci, zai ba ku iri yă kuma ninka shi, yă kuma ƙara girbin adalcinku. 11Za a wadata ku cikin kome, domin dukan karimci, wanda yake haifar da godiya ga Ubanmu ta wurinmu. 12Wannan hidima da kuke yi ba kawai tana biyan bukatun mutanen Ubangiji ba ne, amma tana yalwata cikin godiya mai yawa ga Ubanmu. 13Ta wurin wannan hidima da aka tabbatar, waɗansu za su yabi Ubanmu saboda biyayyarku wajen shaidar bisharar Almasihu, da kuma karimcin rabawarku da su da kowa da kowa. 14Cikin addu'o'insu dominku, za su yi marmarinku, saboda yawan alherin da Ubanmu ya ba ku. 15Godiya ta tabbata ga Ubanmu saboda kyautarsa wadda ba a iya kwatantawa!