Shawulu da 'Ya'yansa sun Mutu a Yaƙi
Yaƙi a Gilbowa ya yi muni. An kashe Yonatan da 'yan'uwansa, maharba sun yi wa Saul rauni, mai ɗaukar makamansa kuwa ya ƙi ya ƙarasa shi, sai ya fāɗi a kan takobinsa. Filistiyawa suka kafa gawarsa a jikin garu; mutanen Yabesh-gileyad suka sauko da ita.
31 1Filistiyawa suka yaƙi Isra'ila; mutanen Isra'ila kuwa suka gudu daga gare su, suka fāɗi, suka mutu a kan Dutsen Gilbowa. 2Filistiyawa suka cim ma Shawulu da 'ya'yansa, suka kuma kashe Yonatan, da Abinadab, da Malki-Shuwa, 'ya'yan Shawulu. 3Yaƙin ya tsananta ƙwarai a kan Shawulu. Maharba suka same shi, suka kuwa ji masa mummunan rauni. 4Shawulu ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zāre takobinka ka soke ni, don kada waɗannan marasa kaciya su zo su soke ni, su wulaƙanta ni.” Amma mai ɗaukar makamansa ya ƙi, gama tsoro ya kama shi ƙwarai. Saboda haka Shawulu ya ɗauki takobinsa ya fāɗa a kansa. 5Da mai ɗaukar makamansa ya ga Shawulu ya mutu, shi ma sai ya fāɗa a kan takobinsa ya mutu tare da shi. 6Saboda haka Shawulu ya mutu a wannan rana, shi da 'ya'yansa uku, da mai ɗaukar makamansa, da dukan mutanensa.
7Da mutanen Isra'ila da suke a ƙetaren kwari da kuma a ƙetaren Urdun suka ga sojojin Isra'ila sun gudu, Shawulu kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka watsar da garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu. 8Washegari, Filistiyawa suka zo domin su washe matattu, sai suka tarar da Shawulu da 'ya'yansa uku sun fāɗi a kan Dutsen Gilbowa. 9Suka fille masa kai, suka tuɓe makamansa, suka kuma aika da manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa domin su kai labari a haikalin gumakansu da kuma cikin mutane. 10Suka ajiye makamansa a haikalin Ashtarot, suka kuma manne gawarsa a katangar Bet-shan. a a v10 Ashtarot wata gunkiya ce ta Kan'aniyawa; ajiye makaman Shawulu a haikalinta ita ce hanyar da Filistiyawa suka bi domin su dangana nasarar ga allolinsu.
11Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, 12sai dukan jarumawansu suka yi tafiya dukan dare, suka ɗauko gawar Shawulu da gawawwakin 'ya'yansa daga katangar Bet-shan, suka kawo su Yabesh, suka kuma ƙone su a can. 13Suka ɗauki ƙasusuwansu, suka binne su a ƙarƙashin itacen kirya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.