Jingina da Alkawura
Gargaɗi huɗu da ba su da alaƙa. Ka fita nan da nan daga lamunin da ka yi wa maƙwabci ba tare da tunani ba. Ka dubi tururuwa idan ba ka iya tashi daga gado ba. Ka yi hankali da mai tayar da fitina mai ƙyafta ido yana yin alama. Abubuwa bakwai da Ubanmu yake ƙi. Sa'an nan zina kuma, kamar wuta da aka ɗauka a cikin rigarka.
6 1Ɗana, in ka ba da jingina domin maƙwabcinka, in ka yi alkawari ta hannu domin baƙo, 2ka shiga tarko ta maganar bakinka, an kama ka ta maganar bakinka. 3To, ka yi haka, ɗana, ka kuɓutar da kanka, gama yanzu kana hannun maƙwabcinka ne: ka tafi, ka ƙasƙantar da kanka, ka kuma roƙi maƙwabcinka. 4Kada ka bari idanunka su yi barci, kada ka bari fatan idanunka su yi gyangyaɗi. 5Ka kuɓutar da kanka kamar barewa daga hannu, kamar tsuntsu daga hannun mafarauci.
6Ka je wurin tururuwa, kai rago; ka lura da hanyoyinta ka zama mai hikima. 7Ba tare da shugaba, ko jami'i, ko mai mulki ba, 8Takan tanadi abincinta a lokacin rani, takan kuma tara abincinta a lokacin girbi.
9Har yaushe za ka kwanta a nan, kai rago? Yaushe za ka tashi daga barcinka? 10Ɗan barci kaɗan, ɗan gyangyaɗi kaɗan, ɗan naɗe hannu kaɗan domin hutawa, 11sa'an nan talauci zai auko maka kamar ɗan fashi, rashi kuma kamar mai ɗauke da makami.
12Mutumin banza, mugun mutum, yana yawo da karkatacciyar magana, 13yana ƙyifta ido, yana nuni da ƙafafunsa, yana alama da yatsotsinsa, 14da karkatacciyar zuciya yana ƙulla mugunta, kullum yana zuga faɗa; 15saboda haka masifa za ta auko masa farat ɗaya; nan take zai karye, ba kuwa za a iya warkar da shi ba.
16Akwai abubuwa shida da Ubanmu yake ƙi, har bakwai da suke abin ƙyama a gare shi: 17idanun girman kai, harshen ƙarya, da hannuwan da suke zub da jinin marar laifi, 18zuciyar da take ƙulla mugayen shirye-shirye, ƙafafun da suke garaje zuwa ga mugunta, 19mai shaidar ƙarya wanda yake numfasa ƙarairayi, da wanda yake zuga faɗa a tsakanin 'yan'uwa.
Maganar Ubanka, Garkuwarka
20Ɗana, ka kiyaye umarnin ubanka, kada kuma ka yashe koyarwar mahaifiyarka. 21Ka ɗaura su a zuciyarka kullum; ka rataya su a wuyanka. 22Sa'ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa'ad da kake kwanciya, za su tsare ka; sa'ad da ka farka kuwa, za su yi magana da kai. 23Gama umarni fitila ne, koyarwa kuma haske ne, tsautawar horo kuwa ita ce hanyar rai, 24domin su kiyaye ka daga muguwar mace, daga harshe mai sulɓi na mazinaciya.
25Kada ka yi sha'awar kyanta a zuciyarka, kada kuma ka bari ta kama ka da gashin idonta; 26gama kuɗin karuwa gurasa ɗaya ne kaɗai, amma mace mai aure tana farautar rai mai daraja. 27Mutum zai iya ɗaukar wuta a ƙirjinsa, tufafinsa kuma ba su ƙone ba? 28Ko mutum zai iya tafiya a kan garwashin wuta, ƙafafunsa kuma ba su ƙone ba? 29Haka yake ga wanda yake kwana da matar maƙwabcinsa; duk wanda ya taɓa ta ba zai kuɓuta daga hukunci ba.
30Mutane ba sa reni ɓarawo in ya yi sata domin yă ƙoshi sa'ad da yake jin yunwa, 31amma in an kama shi, zai biya ninki bakwai; zai ba da dukan dukiyar gidansa. 32Wanda yake zina ba shi da hankali; wanda yake yin haka yana hallaka kansa. 33Zai sami raunuka da kunya, kuma ba za a shafe kunyarsa ba.
34Gama kishi yakan sa mutum fushi, ba kuwa zai nuna jinƙai a ranar sakayya ba. 35Ba zai karɓi wata diyya ba; zai ƙi, ko da rashawa ta yi yawa ƙwarai.