Bildad Ya Sāke Magana
Jawabin ƙarshe na Bildad aya shida ne, babu kuma abin da ya rage a cikinsa sai nisa: mulki na Allah ne, har wata da taurari ba su da tsarki a gabansa, to, mene ne mutum? Tsutsa, ɗan tsutsa. Hujjar abokan ta ƙare da kalmomi.
Babi na 25.
25 1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa ya ce, 2“Mulki da razana nasa ne; yana kafa zaman lafiya a can samansa. 3Ko akwai mai iya ƙidaya rundunoninsa? Ashe, haskensa ba ya hudowa a kan kowa ba? 4To, yaya mutum mai mutuwa zai zama mai adalci a gaban Allah? Yaya wanda mace ta haifa zai zama mai tsarki? 5Duba, har wata ma ba ya haske, taurari kuma ba su da tsarki a idanunsa; 6balle fa mutum mai mutuwa, wanda yake tsutsa, da kuma ɗan adam, wanda yake tsutsar ƙasa!”