Rikicin da Kwaɗayi ke Haifarwa
Faɗa yana fitowa daga sha'awoyin da suke yaƙi a ciki; ba su da shi domin ba sa roƙo, sa'ad da kuma suka roƙa, suna roƙo ba daidai ba. Abota da duniya gāba ce da Ubanmu, amma yana ƙara ba da alheri. Ku matso kusa da shi, ku daina shirya gobe kamar rai ba hazo ba ne.
4 1Daga ina ne yaƙe-yaƙe da faɗe-faɗe a tsakaninku suke tasowa? Ba sha'awoyinku da suke yaƙi a cikinku ba ne? 2Kuna marmari, ba ku da shi—sai ku yi kisa. Kuna kwaɗayi, ba za ku iya samu ba—sai ku yi faɗa da yaƙi. Ba ku da shi domin ba ku roƙa ba. 3Kuna roƙo, ba ku kuwa samu ba, domin kuna roƙo da mugun nufi, don ku ɓata shi a kan jin daɗin kanku. 4Ya ku mazinata! Ba ku sani ba ne cewa abota da duniya gāba ce da Ubanmu? Duk wanda ya zaɓi yă zama abokin duniya, ya mai da kansa maƙiyin Ubanmu. 5Ko kuwa a banza Nassi yake magana, yana cewa ruhun da ya sa a cikinmu yana marmari da kishi? 6Amma yana ba da alheri mafi yawa. Shi ya sa Nassi ya ce, “Ubanmu yana gāba da masu girman kai, amma yana ba da alheri ga masu tawali'u.”
7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Ubanmu. Ku tsaya wa Iblis, zai kuwa gudu daga gare ku. 8Ku matso kusa da Ubanmu, shi kuma zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ya ku masu zunubi; ku tsarkake zukatanku, ya ku masu zuciya biyu. 9Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki, ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku zuwa makoki, farin cikinku kuma zuwa ɓacin rai. 10Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubanmu, shi kuwa zai ɗaukaka ku.
11'Yan'uwa, kada ku zargi juna. Duk wanda ya zargi ɗan'uwansa, ko ya hukunta shi, yana zargin doka ne, yana kuma hukunta ta. Amma in kana hukunta doka, kai ba mai kiyaye ta ba ne—kai mai hukunta ta ne. 12Guda ɗaya ne kaɗai mai ba da doka da kuma yin hukunci—shi mai iya ceto ne ko hallakarwa. Kai fa, wane ne kai da za ka hukunta maƙwabcinka?
Kada Ku Yi Fahariya a Kan Gobe
13Yanzu fa, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu tafi wannan birni ko waccan, mu zauna shekara guda, mu yi ciniki, mu kuma yi riba.” 14Ba ku san abin da gobe za tă kawo ba. Mene ne ranku? Gama ku hazo ne, da ake gani na ɗan lokaci, sa'an nan yă ɓace. 15A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubanmu ya yarda, za mu rayu, mu kuma yi wannan ko waccan.” 16Amma yadda yake, kuna taƙama cikin girman kanku. Dukan irin wannan taƙama mugunta ce. 17Saboda haka, duk wanda ya san nagarta da ya kamata yă yi, bai kuwa aikata ta ba, zunubi ne a gare shi.