Mafaka ga Korarru
'Yan gudun hijirar Mowab suna kaɗawa kamar sheƙar da aka watsar, an kuma ce musu su fake a inuwar Sihiyona, inda aka miƙa kursiyin ƙaunar alkawari. Amma girmankan Mowab fahariya ce ta banza, addu'o'insa a masujada kuma ba za su yi nasara ba. Ubanmu ya faɗa; duk da haka annabin yana kuka.
16 1Ku aika da raguna wa mai mulkin ƙasar, daga Sela ta hanyar jeji, zuwa dutsen 'yar Sihiyona. 2Kamar tsuntsaye masu firfitawa, kamar sheƙar da aka watsar, haka 'yan matan Mowab suke a mashigin Arnon. 3Ku ba da shawara; ku yi adalci; ku mai da inuwarku kamar dare da tsakar rana. Ku ɓoye korarru; kada ku ci amanar mai gudun hijira. 4Bari korarruna su zauna a cikinku, ya Mowab; ku zama musu mafaka daga mai hallakarwa. Sa'ad da mai danniya ya ƙare, hallaka kuma ta daina, masu tattakawa kuma suka ɓace daga ƙasar, 5sa'an nan za a kafa gadon sarauta cikin madawwamiyar ƙauna, wani kuma zai zauna a kansa cikin aminci, a cikin tentin Dawuda, wanda yake yin shari'a yana neman gaskiya, mai saurin aikata adalci. 6Mun ji labarin girman kan Mowab—yadda yake mai tsananin girman kai—da fariyarsa, da girman kansa, da hasalarsa; fahariyarsa a banza take. 7Saboda haka bari Mowab ya yi kuka saboda Mowab; bari kowa ya yi kuka. Ku yi makoki, kun karaya ƙwarai, saboda wainar zabibi na Kir-hareset. 8Gama gonakin Heshbon sun yanƙwane, da kuringar inabi ta Sibma; masu mulkin al'ummai sun sare zaɓaɓɓun rassanta, waɗanda suka kai har Yazer suka kuma bazu zuwa cikin jeji; tohonta ya yaɗu ya kuma ƙetare teku. 9Saboda haka ina kuka tare da kukan Yazer saboda kuringar inabi ta Sibma; ina jiƙe ku da hawayena, ya Heshbon da Eleyale, gama a kan 'ya'yan bazaranku da girbinku ihun yaƙi ya auka. 10An kawar da murna da farin ciki daga gona mai albarka, a cikin gonakin inabi kuma ba a rera waƙoƙi, ba a tā da sowa ta murna. Ba wanda yake matsar da ruwan inabi a wuraren matsi; na kawo ƙarshen ihu. 11Saboda haka zuciyata tana nishi kamar molo saboda Mowab, cikin cikina kuma saboda Kir-heres. a a v11 Zuciyar Ubanmu tana nishi har ma a kan Mowab — baƙin cikinsa yakan kai ga kowace al'umma da hukuncinsa ya taɓa. 12Sa'ad da Mowab ya gabatar da kansa, sa'ad da ya gajiyar da kansa a kan tsauni ya kuma zo wurinsa mai tsarki domin yă yi addu'a, ba zai yi nasara ba. b b v12 'Tsauni' wurin sujada ne a kan tudu da ake amfani da shi don bautar gumaka da yin hadaya.
13Wannan ita ce maganar da Ubanmu ya yi game da Mowab a dā.
14Amma yanzu Ubanmu ya yi magana, “A cikin shekaru uku, kamar shekarun ɗan kwadago, za a rena ɗaukakar Mowab, duk da yawan jama'arsa mai yawa; sauran ragowar kuma za su zama kaɗan ƙwarai da rarauna.”