Ƙarfafawa ta Wurin Alheri don Jimiri
Bulus ya gaya wa Timoti ya ɗebo ƙarfinsa daga alheri, ya kuma miƙa koyarwar ga amintattun mutane waɗanda za su iya koya wa wasu. Soja, ɗan wasa, manomi — kowane misali game da jure wahala ne. Gardama kan kalmomi ba ta da amfani; ka yi gyara da tawali'u, domin Ubanmu yana iya ba da tuba.
2 1Saboda haka, ɗana, ka sami ƙarfinka daga alherin da yake cikin Almasihu Yesu. 2Abin da ka ji daga gare ni a gaban shaidu masu yawa, ka danƙa shi ga mutane amintattu, waɗanda za su iya koya wa waɗansu su ma. 3Ka ɗauki rabonka na shan wahala kamar soja nagari na Almasihu Yesu. 4Ba sojan da yake kan aiki da yakan shiga harkokin rayuwar talakawa ba, gama yana so yă gamshi wanda ya ɗauke shi aikin soja. 5Ɗan wasa kuma ba a ba shi kambi sai ya yi gasa bisa ƙa'ida. 6Ya dace manomi mai aiki tuƙuru yă zama na farko da zai sami rabo a cikin amfanin gona. 7Ka yi tunani a kan abin da nake faɗa, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin kome.
8Ka tuna da Yesu Almasihu, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, kamar yadda bisharata ta faɗa, 9wadda nake shan wahala saboda ita, har aka daure ni da sarƙa kamar mai laifi. Amma ba a daure maganar Ubanmu da sarƙa ba! 10Saboda haka ina jimre da kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceto wanda yake cikin Almasihu Yesu, tare da ɗaukaka madawwamiya. 11Wannan magana tabbatacciya ce: In mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi; 12in mun jimre, za mu kuma yi mulki tare da shi; in mun yi musunsa, shi ma zai yi musunmu; 13in ba mu da aminci, shi kuwa yana nan da aminci, domin ba ya iya yin musun kansa ba.
Ma'aikacin da Uba ya Amince da shi
14Ka tuna musu da waɗannan abubuwa, ka kuma gargaɗe su a gaban Ubanmu kada su yi gardama a kan kalmomi—wannan ba ya da amfani, yana kuma ɓata waɗanda suke ji.
15Ka yi iyakar ƙoƙarinka ka gabatar da kanka ga Ubanmu a matsayin wanda aka amince da shi, ma'aikaci wanda ba shi da abin kunya, yana sarrafa maganar gaskiya yadda ya dace. 16Amma ka guji surutan banza marasa tsoron Allah, gama hakan yana ƙara kai mutane cikin mugunta, 17maganarsu kuwa za ta yaɗu kamar ciwon da yake cin naman jiki. A cikinsu akwai Himinawus da Filitus, 18waɗanda suka kauce daga gaskiya, suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma rushe bangaskiyar waɗansu mutane. 19Duk da haka tushen Ubanmu mai ƙarfi yana nan tsaye, an kuma hatimce shi da waɗannan kalmomi, “Shi ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda yake ambaton sunansa, sai yă rabu da mugunta.”
20A cikin babban gida akwai kwanoni, ba na zinariya da azurfa kaɗai ba, har ma na itace da na laka—waɗansu don girma, waɗansu kuma don wulaƙanci. 21Saboda haka in wani ya tsarkake kansa daga waɗannan, zai zama kwanon girma: tsattsarka, mai amfani ga Maigida, a shirye don kowane kyakkyawan aiki.
22Ka guji sha'awace-sha'awacen ƙuruciya; ka nemi adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da salama, tare da waɗanda suke kiran Ubangiji da zuciya mai tsabta. 23Ka ƙi shiga gardandami na wauta da jahilci; ka san suna haifar da faɗace-faɗace. 24Bawan Ubangiji kuwa bai kamata yă zama mai neman faɗa ba, sai dai yă zama mai sauƙin hali ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri sa'ad da aka yi masa laifi. 25Yana gyara masu gāba da shi cikin tawali'u. Watakila Ubanmu zai ba su tuba su san gaskiya, 26ta haka kuma su farka, su tsere daga tarkon Iblis, wanda ya kama su bayi domin su aikata nufinsa.