Wanda Yake Riƙe da Taurari
Yesu ya faɗi wasiƙu huɗu a rubuta. Afisa tana aiki tuƙuru amma ta bar ƙaunar da take da ita da farko. Simirna matalauciya ce, ana gab da sa ta a kurkuku. Birgamus tana haƙuri da koyarwar Bala'amu, Tiyatira tana haƙuri da Yezebel. An ambaci kowane laifi, sa'an nan alkawarin itacen rai a aljannar Ubanmu.
2 1“Ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiya a Afisa cewa, Wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama, yana kuma tafiya tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya, ga abin da yake faɗa,
2“Na san ayyukanka, da wahalarka, da jimirinka, da kuma cewa ba ka iya haƙuri da mugaye; ka gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuma same su maƙaryata. 3Ka yi haƙuri ka kuma jure saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba. 4Amma ina da abu guda a kanka, ka watsar da ƙaunarka ta farko. 5Saboda haka ka tuna inda ka fāɗo daga gare shi; ka tuba ka kuma yi ayyukanka na farko. In ba haka ba, zan zo maka in cire alkukin fitilarka daga wurinsa—sai dai in ka tuba. 6Amma ga abin da kake da shi, kana ƙin ayyukan Nikolawa, waɗanda ni ma nake ƙi. 7Duk mai kunne, sai ya ji abin da Ruhu Mai Tsarki yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Ga wanda ya yi nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai da yake cikin aljannar Ubanmu.
Na Farko da Na Ƙarshe
8“Ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiya a Simirna cewa, Wanda yake na farko da na ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke rayuwa, ga abin da yake faɗa,
9“Na san wahalarka da talaucinka—duk da haka kai mai arziki ne—da kuma ɓatan suna daga waɗanda suke ce da kansu Yahudawa alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai majami'ar Shaiɗan ce. 10Kada ka ji tsoron abin da za ka sha. Iblis zai jefa waɗansunku a kurkuku domin a gwada ku; za ku sha wahala har kwana goma. Ka yi aminci har ga mutuwa, zan kuwa ba ka rawanin rai. 11Duk mai kunne, sai ya ji abin da Ruhu Mai Tsarki yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Wanda ya yi nasara, mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba.
Takobi Mai Kaifi Gefe Biyu
12“Ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiya a Birgamus cewa, Ga maganar wanda yake da takobi mai kaifi gefe biyu,
13“Na san inda kake zama—inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kana riƙe da sunana, ba ka kuma taɓa yin mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a lokacin da aka kashe Antipas, amintaccen mai shaidata, a cikinku, inda Shaiɗan yake zama. 14Amma ina da abubuwa kaɗan a kanka, akwai waɗansu a wurin da suke riƙe da koyarwar Bala'amu. Shi ne ya koya wa Balak yă sa abin tuntuɓe a gaban Isra'ila, su ci abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci. 15Haka kai ma kana da waɗansu da suke riƙe da koyarwar Nikolawa. 16Saboda haka ka tuba. In ba haka ba, ba da daɗewa ba zan zo maka in yāƙi waɗanda suke riƙe da ita da takobin bakina. 17Duk mai kunne, sai ya ji abin da Ruhu Mai Tsarki yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Ga wanda ya yi nasara, zan ba shi manna ɓoyayye da kuma farin dutse wanda a kansa aka rubuta sabon suna wanda babu wanda ya sani sai wanda ya karɓe shi.
Idanu Kamar Harshen Wuta
18“Ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiya a Tiyatira cewa, Ɗan Ubanmu, wanda idanunsa suke kamar harshen wuta, ƙafafunsa kuma kamar tagullar da aka goge, ga abin da yake faɗa,
19“Na san ayyukanka—ƙaunarka, da bangaskiyarka, da hidimarka, da jimirinka—da kuma cewa ayyukanka na ƙarshe sun fi na farko yawa. 20Amma ina da abu guda a kanka, kana haƙuri da macen nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, tana koyarwa tana kuma ɓad da bayina su shiga fasikanci da kuma cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya. 21Na ba ta lokaci tă tuba, amma ba ta so tă tuba daga fasikancinta ba. 22Zan jefa ta a gadon ciwo, in kuma jefa waɗanda suke yin zina da ita cikin azaba mai tsanani, sai dai in sun juya daga ayyukanta. 23Zan kuma kashe 'ya'yanta. Sa'an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne wanda yake bincika tunani da zuciya, zan kuma sāka wa kowannenku bisa ga ayyukansa. 24Amma ga sauranku da kuke a Tiyatira, waɗanda ba su riƙe da wannan koyarwa ba, waɗanda ba su koyi abin da ake kira zurfafan al'amuran Shaiɗan ba, ina gaya muku, ba zan ɗora muku wani kaya dabam ba. 25Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi kam har in zo. 26Wanda ya yi nasara, ya kuma kiyaye ayyukana har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al'ummai, 27zai kuma yi mulkinsu da sandar ƙarfe, yă farfasa su kamar tukwanen yumɓu—kamar yadda ni ma na karɓi iko daga wurin Ubana. 28Zan kuma ba shi tauraron asubahi. 29Duk mai kunne, sai ya ji abin da Ruhu Mai Tsarki yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”