Daga Ƙura zuwa Teburin Sarakuna
Tambayar ita ce yadda Ubanmu, da yake zaune can sama ƙwarai, yake ganin har ƙasa can. Amsar ita ce abin da yake yi sa'ad da ya sunkuya: yana ɗaga mabaraci daga juji ya zaunar da shi tare da sarakuna, yana kuma ba wa mace marar haihuwa gida cike da 'ya'ya.
113 1Halleluya! Ku yabe shi, ku bayin Ubanmu; ku yabi sunan Ubanmu. 2Albarka ta tabbata ga sunan Ubanmu, daga yanzu har abada abadin. 3Daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta, ya kamata a yabi sunan Ubanmu. 4An ɗaukaka Ubanmu bisa dukan al'ummai, ɗaukakarsa kuwa ta fi sammai. 5Wane ne kamar Ubanmu, wanda yake zaune a can bisa, 6wanda yake sunkuyowa domin yă dubi sammai da ƙasa? 7Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mabukaci daga juji, 8domin yă zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan jama'arsa. 9Yakan zaunar da macen da ba ta haihuwa a gidanta tă zama uwa mai farin ciki da 'ya'ya. Halleluya!