Gileyad: Kyakkyawar Ƙasa don Dabbobi
Ra'ubainu da Gad suna son kyakkyawan wurin kiwo a gabashin Urdun, Musa kuma ya ji sāke-sāken ƙin da kakanninsu suka yi na shiga ƙasar da Ubanmu ya bayar. Suka yarda su haye da makamai su yi yaƙi a gaban 'yan'uwansu har sai an mallaki ƙasar, sa'an nan kaɗai su koma gida.
32 1'Ya'yan Ra'ubainu da 'ya'yan Gad suna da garkuna masu yawan gaske na dabbobi. Da suka ga ƙasar Yazer da ƙasar Gileyad, sai suka lura ta dace da dabbobi ƙwarai. 2'Ya'yan Gad da 'ya'yan Ra'ubainu suka zo suka ce wa Musa, da Eleyazar firist, da shugabannin jama'a, 3“Ataros, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo, da Beyon, 4ƙasar da Ubanmu ya ci da yaƙi a gaban jama'ar Isra'ila, ƙasa ce mai dacewa da dabbobi, bayinka kuwa suna da dabbobi.” 5Suka ce, “In mun sami tagomashi a gabanka, ka ba wa bayinka wannan ƙasa ta zama gādonsu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
6Musa ya ce wa 'ya'yan Gad da na Ra'ubainu, “'Yan'uwanku za su tafi yaƙi ku kuwa ku zauna a nan? 7Don me kuke karya wa Isra'ila zuciya su haye zuwa ƙasar da Ubanmu ya ba su? 8Haka ubanninku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya su ga ƙasar. 9Suka hau zuwa Kwarin Eshkol, suka ga ƙasar, sa'an nan suka karya wa Isra'ilawa zuciya don kada su shiga ƙasar da Ubanmu ya ba su. 10Fushin Ubanmu kuwa ya ƙuna a wannan rana, sai ya rantse, yana cewa, 11Lalle mutanen da suka fito daga Masar, masu shekara ashirin zuwa sama, ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba wa Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙubu ba, domin ba su bi ni da zuciya ɗaya ba. 12Sai dai Kalibu ɗan Yefunne Keniziye da Yoshuwa ɗan Nun, gama sun bi Ubanmu da zuciya ɗaya. 13Fushin Ubanmu ya ƙuna a kan Isra'ila, sai ya sa suka yi ta yawo a jeji shekara arba'in, sai da dukan tsararraki da suka aikata mugunta a gaban Ubanmu suka mutu.
14Yanzu kuwa ga ku, kun tashi a maimakon ubanninku, zuriyar masu zunubi, kuna ƙara zafin fushin Ubanmu a kan Isra'ila! 15In kuka juya, kuka bar binsa, zai sāke yashe su a jeji, ku kuwa za ku hallaka dukan wannan jama'a.”
16Suka zo wurinsa suka ce, “Za mu gina garke domin dabbobinmu a nan, da birane domin 'ya'yanmu. 17Amma mu za mu ɗauki makamai, a shirye mu sha gaban Isra'ilawa sai mun kai su wurinsu, 'ya'yanmu kuwa su zauna a biranen da suke da katanga, lafiya daga mazaunan ƙasar. 18Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra'ila ya sami gādonsa. 19Ba za mu yi gādo tare da su a hayin Urdun da gaba ba, da yake gādonmu ya zo mana a wannan gefen Urdun, wajen gabas.”
20Musa ya ce musu, “In kuka yi haka, in kuka ɗauki makamai a gaban Ubanmu don yaƙi, 21kowane mai ɗauke da makami a cikinku kuwa ya haye Urdun a gaban Ubanmu sai ya kori abokan gābansa daga gabansa, 22ƙasar kuwa ta zama ƙarƙashi a gaban Ubanmu, bayan haka za ku iya komawa, ku rabu da alhakin da yake kanku gare shi da kuma ga Isra'ila, wannan ƙasa kuwa za ta zama gādonku a gaban Ubanmu. 23Amma in ba ku yi haka ba, ga shi, kun yi wa Ubanmu zunubi, ku kuma sani, zunubinku zai same ku. 24Ku gina birane domin 'ya'yanku ƙanana, da garke domin tumakinku, ku kuma yi abin da bakinku ya alkawarta.”
25'Ya'yan Gad da na Ra'ubainu suka ce wa Musa, “Bayinka za su yi yadda ranka yă daɗe ya umarta. 26'Ya'yanmu, da matanmu, da garkunanmu, da dukan dabbobinmu za su zauna a can a biranen Gileyad, 27amma bayinka, kowane mutum mai ɗauke da makamin yaƙi, za su haye a gaban Ubanmu zuwa yaƙi, yadda ranka yă daɗe ya faɗa.”
28Saboda haka Musa ya umarci Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra'ila game da su. 29Musa ya ce musu, “In 'ya'yan Gad da na Ra'ubainu suka haye Urdun tare da ku, kowane mutum mai ɗauke da makamin yaƙi a gaban Ubanmu, ƙasar kuwa ta zama ƙarƙashi a gabanku, to, ku ba su Gileyad ta zama gādonsu. 30Amma in ba za su haye da makamai tare da ku ba, to, dole su sami gādo a cikinku a ƙasar Kan'ana.”
31'Ya'yan Gad da na Ra'ubainu suka amsa suka ce, “Za mu yi yadda Ubanmu ya faɗa wa bayinka. 32Mu da kanmu za mu haye da makamai a gaban Ubanmu zuwa ƙasar Kan'ana, gādonmu kuwa zai kasance namu a hayin Urdun.”
33Sai Musa ya ba su, wato 'ya'yan Gad, da 'ya'yan Ra'ubainu, da rabin kabilar Manasse ɗan Yusufu, mulkin Sihon sarkin Amoriyawa da mulkin Og sarkin Bashan, wato ƙasar, da biranenta, da yankunanta, da kuma biranen ƙasar da suke kewaye. 34'Ya'yan Gad kuwa suka gina Dibon, da Ataros, da Arower, 35da Atros-shofan, da Yazer, da Yogbeha, 36da Bet-nimra, da Bet-haran, wato birane masu katanga da garken tumaki. 37'Ya'yan Ra'ubainu kuwa suka gina Heshbon, da Eleyale, da Kiriyatayim, 38da Nebo, da Ba'al-meyon (wanda aka sāke masa suna), da Sibma, sun ba wa biranen da suka sāke ginawa sababbin sunaye. 39'Ya'yan Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori Amoriyawan da suke zaune a can. 40Saboda haka Musa ya ba Makir ɗan Manasse Gileyad, shi kuwa ya zauna a cikinta. 41Yayir ɗan Manasse kuwa ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kira su Hawwot-yayir. 42Noba kuwa ya tafi ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kira ta Noba, bisa sunansa.