Ranar da Ubanmu zai Yi Aiki
Makoma biyu a rana ɗaya da Ubanmu zai yi aiki: masu girmankai za su ƙone kamar ciyawar kara, amma waɗanda suke tsoron sunansa za su fita suna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka saki daga turke. An yi alkawarin Iliya zai fara zuwa, a aiko shi ya juyo da zukatan ubanni ga 'ya'ya, da zukatan 'ya'ya ga ubanni.
4 1Ga shi, rana tana zuwa, mai ƙuna kamar tanderu, sa'ad da dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta za su zama tattaka; ranan nan za ta ƙone su, in ji Uban rundunonin Sama, har ba za ta bar musu ko saiwa ko reshe ba. 2Amma gare ku masu tsoron sunana, ranar adalci za ta fito mai warkarwa a fikafikanta, za ku kuma fita kuna tsalle kamar maruƙa daga turke. 3Za ku tattake mugaye, gama za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan yi aiki, in ji Uban rundunonin Sama.
4“Ku tuna da shari'ar bawana Musa, ƙa'idodi da hukunce-hukuncen da na umarce shi da su a Horeb domin dukan Isra'ila.
5Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin ranar Ubanmu mai girma da ban tsoro ta zo. a a v5 Yesu ya shaida cewa Yohanna Mai Baftisma shi ne Iliya da aka yi alkawari a nan, wanda ya zo domin yă shirya zukata saboda shi (Matta 11:14; 17:10-13). 6Zai juya zukatan iyaye ga 'ya'yansu, da zukatan 'ya'ya ga iyayensu, don kada in zo in hallaka ƙasar ƙaƙaf.”