Uba Ya Janye Kansa daga Marasa Aminci
An kira firistoci da sarki da al'umma duka. Ayyukansu ba za su bar su su komo ba, kuma sa'ad da suka je nema da garkunan tumaki da na shanu, Ubanmu ya riga ya janye. Ya kira kansa ruɓa ga Yahuza da zaki ga Ifraimu, sa'an nan ya tafi har sai wahala ta kore su su komo.
5 1Ku ji wannan, ku firistoci! Ku mai da hankali, gidan Isra'ila! Ku saurara, gidan sarki! Gama hukuncin dominku ne, domin kun zama tarko a Mizfa, kuma raga da aka shimfiɗa a kan Tabor.
2“'Yan tawaye sun nutse cikin kisankai, amma zan horar da dukansu. 3Na san Ifraimu, Isra'ila kuma ba a ɓoye yake daga gare ni ba; yanzu kuwa, Ifraimu, ka yi karuwanci, Isra'ila kuma ta ƙazantu.
4“Ayyukansu ba za su bar su su koma wurin Ubansu ba, gama ruhun karuwanci yana a cikinsu, kuma ba su san Ubanmu ba. 5Girman kan Isra'ila yana ba da shaida a kansa; Isra'ila da Ifraimu sun yi tuntuɓe cikin zunubinsu; Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su. 6Da garkunan tumakinsu da na shanunsu za su tafi neman Ubanmu, amma ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su. 7Sun yi rashin aminci ga Ubanmu, gama sun haifi 'ya'yan shege. Yanzu sabon wata zai cinye su tare da gonakinsu.
8“Ku busa ƙaho a Gibeya, ku busa kakaki a Rama. Ku tā da ƙarar yaƙi a Bet-awen; ka waiwaya baya, Benyamin! 9Ifraimu zai zama kufai a ranar hukunci; a cikin kabilan Isra'ila na sanar da abin da yake tabbatacce. 10Sarakunan Yahuda sun zama kamar waɗanda suke matsar da shaidar iyaka; a kansu zan zubar da fushina kamar ruwa. 11An danne Ifraimu, an ragargaza shi cikin hukunci, domin ya nace ga bin gumaka marasa amfani. 12Saboda haka ni kamar asu ne ga Ifraimu, kuma kamar ruɓa ga gidan Yahuda.
13“Ifraimu ya ga cutarsa, Yahuda kuma ya ga gyambonsa; sai Ifraimu ya ruga zuwa Assuriya, yana neman taimako daga babban sarkinta. Amma sarkin nan ba ya iya warkar da ku, ko ya warkar da gyambonku mai ruɓewa. 14Gama zan zama kamar zaki ga Ifraimu, kuma kamar ɗan zaki ga gidan Yahuda. Ni kaina zan yayyage in tafi; zan ɗauke su, kuma babu wanda zai ceto. 15Zan sāke komawa wurina, sai sun yarda da laifinsu su kuma nemi fuskata; cikin damuwarsu za su neme ni da gaske.”