Umarnan Uba
A rana ta fari ta shekara aka kafa kome, aka shafe shi, aka sa shi a wurinsa, aka wanke Haruna da 'ya'yansa aka sa musu tufafi. Sa'an nan girgijen ya rufe alfarwar, ɗaukakar Ubanmu kuma ta cika ta har Musa bai iya shiga ba. Daga nan gaba, girgijen ne yake yanke lokacin da za su tashi.
40 1Sai Ubanmu ya yi magana da Musa, ya ce,
2“Ka kafa tabanakul, wato tentin sujada, a ranar farko ta watan farko. 3Ka sa akwatin shaida a cikinsa, ka kuma rufe akwatin da labule. 4Ka shigo da tebur, ka shirya kayansa, ka shigo da alkukin fitila, ka kuma kunna fitilunsa. 5Ka sa bagaden turare na zinariya a gaban akwatin shaida, ka kuma sa labulen ƙofa a mashigin tabanakul. 6Ka sa bagaden hadaya ta ƙonawa a gaban mashigin tabanakul, wato tentin sujada, 7ka kuma sa daro tsakanin tentin sujada da bagade, ka zuba ruwa a cikinsa. 8Ka kafa fili kewaye da shi duka, ka kuma rataya labulen ƙofa a ƙofar filin.
9“Ka ɗauki man shafawa, ka shafe tabanakul da kome da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayansa, zai kuwa zama mai tsarki. 10Ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayan aikinsa; ka keɓe bagaden, bagaden kuwa zai zama mai cikakken tsarki. 11Ka shafe daro da gindinsa, ka kuma keɓe shi.
12“Sa'an nan ka kawo Haruna da 'ya'yansa maza zuwa mashigin tentin sujada, ka wanke su da ruwa. 13Ka sa wa Haruna tufafi masu tsarki, ka shafe shi, ka keɓe shi, domin yă yi mini hidima a matsayin firist. 14Ka kawo 'ya'yansa maza, ka sa musu dogayen riguna. 15Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, domin su yi mini aikin firist. Shafawarsu za ta ba su madawwamin aikin firist har tsararraki duka.”
16Musa ya yi kome kamar yadda Ubanmu ya umarce shi. 17A watan farko na shekara ta biyu, a ranar farko ta watan, aka kafa tabanakul. 18Musa ya kafa tabanakul: ya sa kujerunsa, ya kakkafa katakansa, ya sa sandunansa, ya kuma tā da ginshiƙansa. 19Ya shimfiɗa tenti a kan tabanakul, ya kuma sa murfinsa a kai, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 20Ya ɗauki shaida, ya sa ta a cikin akwatin, ya sa sanduna a kan akwatin, ya kuma sa murfin jinƙai a bisa akwatin. 21Ya shigar da akwatin cikin tabanakul, ya rataya labulen kariya, ya kuma rufe akwatin shaida, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 22Ya sa tebur a cikin tentin sujada, a gefen arewa na tabanakul, a bayan labule, 23ya kuma shirya gurasa a kansa a gaban Ubanmu, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 24Ya sa alkukin fitila a cikin tentin sujada, ɗaura da tebur, a gefen kudu na tabanakul, 25ya kuma kafa fitilu a gaban Ubanmu, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 26Ya sa bagaden zinariya a cikin tentin sujada a gaban labule, 27ya kuma ƙona turare mai ƙanshi a kansa, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 28Sa'an nan ya sa labulen ƙofa a mashigin tabanakul. 29Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa a mashigin tabanakul, wato tentin sujada, ya kuma miƙa a kansa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 30Ya sa daro tsakanin tentin sujada da bagade, ya zuba ruwa a cikinsa domin wanki, 31da shi kuwa Musa da Haruna da 'ya'yansa sukan wanke hannuwansu da ƙafafunsu. 32Duk sa'ad da suka shiga tentin sujada ko suka kusaci bagade, sukan yi wanka, kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa. 33Ya kafa fili kewaye da tabanakul da bagade, ya kuma sa labulen ƙofa a ƙofar filin. Ta haka Musa ya gama aikin.
Ɗaukakarsa Ta Cika Tabanakul
34Sai girgije ya rufe tentin sujada, ɗaukakar Ubanmu kuwa ta cika tabanakul. 35Musa bai iya shiga tentin sujada ba, gama girgije ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubanmu kuwa ta cika tabanakul. 36Duk sa'ad da girgije ya tashi daga kan tabanakul, Isra'ilawa sukan kama hanya a kowane matakin tafiyarsu; 37amma in girgije bai tashi ba, ba sa tashi sai ranar da ya tashi. 38Gama girgijen Ubanmu ya rufe tabanakul da rana, da dare kuwa akwai wuta a cikinsa, a bayyane ga dukan gidan Isra'ila a cikin tafiyarsu duka.