Halleluya
Zabura ta ƙarshe fashewar yabo ce ta rufewa ga Ubanmu — wuri mai tsarki da sararin sama, ƙahon rago, garaya, ganga, molaye, sarewa da kuge iri biyu — ba gardama ba roƙo a cikinta. Abin da kaɗai aka ambata a matsayin sharaɗi shi ne numfashi.
150 1Halleluya! Ku yabi Ubanmu a cikin wurinsa mai tsarki; ku yabe shi a sararin samansa mai iko. 2Ku yabe shi saboda manyan ayyukansa; ku yabe shi gwargwadon yawan girmansa. 3Ku yabe shi da busar ƙahon rago; ku yabe shi da garaya da molo. a a v3 Shofar ƙaho ne na rago da ake busawa a bukukkuwa da tarukan Isra'ila — busarsa takan kira mutane su kasa kunne a gaban Ubanmu. 4Ku yabe shi da ganga da rawa; ku yabe shi da kiɗan tsirkiya da sarewa. 5Ku yabe shi da kuge masu amo; ku yabe shi da kuge masu kaɗawa da ƙarfi. 6Bari duk mai numfashi yă yabi Ubanmu. Halleluya!