Sa'ar Hukuncin Ninawa
Kewayewar ta iso: garkuwoyi jajaye, karusai suna gudu kamar walƙiya, an ɓalle ƙofofin kogi, fādar ta rushe, an kwashe sarauniya yayin da kuyanginta suke bugun ƙirjinsu. Assuriya zaki ne wanda ya cika kogonsa da naman da ya yayyage; Uban rundunonin sama ya ce yana gāba da ita.
2 1Mai warwatsawa ya taso miki, Ninawa. Ki tsare kagara, ki yi tsaron hanya, ki ƙarfafa kanki, ki tattara dukan ƙarfinki!
2Gama Ubanmu yana maido da darajar Yakubu, kamar darajar Isra'ila, ko da yake masu washi sun washe su tsaf, suka lalatar da rassansu. a a v2 Ko a cikin littafin hukunci a kan Ninawa, ainihin saƙonsa shi ne Ubanmu yana maido da martabar 'ya'yansa da aka wulaƙanta.
3An rina garkuwoyin jarumawansa ja wur, jarumawa suna saye da jan kaya mai haske; karusai suna ƙyalli kamar wuta a ranar da aka shirya su, ana kuma girgiza māsu na itace. 4Karusai suna ruga a cikin tituna, suna kai da kawowa a dandali; suna kama da fitilu, suna wulga kamar walƙiya. 5Yana kiran hafsoshinsa; suna tuntuɓe yayinda suke tafiya; suna hanzari zuwa katanga, an kuma kafa garkuwar tsaro a wurinta. 6An buɗe ƙofofin kogi, fada kuwa ya rushe. 7An yanke hukunci: an tuɓe ta aka kwashe ta, kuyanginta kuwa suna nishi kamar tantabaru, suna bugun ƙirjinsu. 8Ninawa tana kama da tafki wanda ruwansa yake malalewa. Suna ihu, “Ku tsaya! Ku tsaya!” amma ba wanda ya juyo baya. 9Ku washe azurfa! Ku washe zinariya! Dukiya ba ta da iyaka, yalwar kowane abu mai daraja. 10Wofi da kango da hallaka! Zukata sun narke, gwiwowi suna rawa, azaba ta kama kowane jiki, kowace fuska kuwa ta ɓace launi.
11Ina yanzu kogon zakoki, wurin ciyar da ƙanana zakoki, inda zaki da zakanya suke yawo, da 'ya'yan zaki, babu mai tsoratar da su? 12Zaki ya yayyaga ganima da ta ishe 'ya'yansa, ya kuma shaƙe ganima domin zakanyoyinsa; ya cika maɓuyoyinsa da naman farauta, da kogwanninsa da yagaggen nama.
13“Ga ni, ina gāba da ke,” in ji Uba, Maigadin rundunonin Sama. “Zan ƙone karusanki su koma hayaƙi, takobi kuma zai cinye ƙanana zakokinki. Zan datse ganimarki daga duniya, muryar manzanninki kuwa ba za a ƙara jin ta ba.”