Uba Ya Hukunta Fir'auna
Fir'auna shi ne babban dodon kogi da ke cewa Kogin Nilu nasa ne domin shi ya yi shi. Ubanmu ya sa ƙugiya a muƙamuƙinsa ya ja shi zuwa jeji. Masar ta zama wa Isra'ila kamar iwa mai tsattsagewa. Bayan shekara arba'in tana kufai, za ta komo a matsayin mafi ƙasƙanci cikin mulkoki.
29 1A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta sha biyu ga wata, sai maganar Ubanmu ta zo mini cewa,
2Ɗan mutum, ka fuskanci Fir'auna sarkin Masar, ka yi annabci game da shi da dukan Masar.
3Ka yi magana ka ce, ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa, “Ga shi, ina gāba da kai, Fir'auna sarkin Masar, kai babban dodo da yake kwance a cikin magudanan ruwanka, wanda yake cewa, ‘Kogin Nilu nawa ne; ni na yi shi domin kaina.’ 4Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka, in sa kifin magudanan ruwanka su manne a ɓamɓarorin jikinka; zan jawo ka daga tsakiyar magudanan ruwanka, tare da dukan kifin magudanan ruwanka manne a ɓamɓarorin jikinka. 5Zan jefar da kai cikin jeji, kai da dukan kifin magudanan ruwanka. Za ka fāɗi a fili; ba za a tattara ka ko a tāra ka ba. Na ba da kai abinci ga namun jeji da tsuntsayen sama. 6Sa'an nan dukan mazaunan Masar za su san ni ne Uba, domin sun zama sandar kyauro ga gidan Isra'ila. 7Sa'ad da suka kama ka, sai ka farfashe ka tsage kafaɗunsu; sa'ad kuma da suka jingina a kanka, sai ka karye ka sa ƙafafunsu su raunana.”
8Saboda haka ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa, Ga shi, ina kawo takobi a kanka, zan kuwa kawar da mutum da dabba daga gare ka.
9Ƙasar Masar za ta zama kango da kufai, za su kuma san ni ne Uba—domin Fir'auna ya ce, “Kogin Nilu nawa ne; ni na yi shi.”
10“Saboda haka ina gāba da kai da kuma magudanan ruwanka, zan mai da ƙasar Masar kufai da kango ƙaƙaf, daga Aswan har zuwa iyakar Kush. 11Ƙafar mutum ba za ta ratsa ta ba, ƙafar dabba kuma ba za ta ratsa ta ba; ba wanda zai zauna a cikinta har shekara arba'in. 12Zan mai da ƙasar Masar kango a cikin ƙasashen da suka zama kufai, biranenta kuma su zama kango a cikin biranen da aka washe har shekara arba'in. Zan watsar da Masarawa cikin al'ummai, in warwatsa su cikin ƙasashe.”
13Gama ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa, “Bayan shekara arba'in zan tattara Masarawa daga cikin mutanen da aka watsar da su a cikinsu. 14Zan maido da wadatar Masar, in komar da su ƙasar Fatros, ƙasarsu ta haihuwa, a can kuwa za su zama ƙasƙantacciyar masarauta. 15Za ta zama mafi ƙasƙanci a cikin masaraututa, ba za ta ƙara ɗaukaka kanta bisa al'ummai ba. Zan sa su yi ƙanƙanta sosai har ba za su ƙara mallakar al'ummai ba. 16Masar ba za ta ƙara zama abin dogaron gidan Isra'ila ba, sai dai ta zama abin tunawa da laifinsu duk sa'ad da suka juya gare ta. Sa'an nan za su san ni ne Uba Mai Iko Duka.”
17A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari, a rana ta fari, sai maganar Ubanmu ta zo mini cewa,
18Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babila ya sa sojojinsa su yi faman aiki game da Taya. Kowanne kai ya zama sumul, kowace kafaɗa ta ɓare, duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wata lada daga Taya ba saboda aikin da ya yi game da ita. 19Saboda haka ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa, Yanzu ina ba da ƙasar Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babila. Zai ɗauke dukiyarta, ya kame ganimarta, ya washe abin da za a washe—ladan sojojinsa ke nan. 20Da ladan aikin da ya yi, na ba shi ƙasar Masar, domin sun yi shi saboda ni, in ji Uba Mai Iko Duka.
21A ranar nan zan sa ƙaho yă tsiro wa gidan Isra'ila, in kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa'an nan za su san ni ne Uba. a a v21 Ƙahon da yake tsirowa alama ce ta ƙaruwar ƙarfi da ceto; yana nuni gaba ga ƙahon ceto da Ubanmu ya tā da cikin Yesu, wanda aka haifa daga zuriyar Dawuda.