Ranar Masifa ga Masar
Waƙar kururuwa a kan Masar da abokan ƙawancenta, tana ambaton birni bayan birni, Memfis, Tebes, Felusiyum, Tafanhes, da aka cinna musu wuta ko aka kwashe su bauta. Ubanmu ya riga ya karya hannun Fir'auna, ba kuwa za a ɗaure shi ba, maimakon haka an sa takobin a hannun Babila.
30 1Maganar Ubanmu ta zo mini:
2Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, Maɗaukakin Uba ya ce, “Ku yi kuka, ‘Kaito, ranan nan!’ 3Gama ranar ta yi kusa, ranar Ubanmu ta yi kusa— ranar gizagizai, lokacin masifa ga al'ummai. 4Takobi zai fāɗo wa Masar, azaba kuma za ta kasance a Kush sa'ad da waɗanda aka kashe suka fāɗi a Masar, sa'ad da suka kwashe dukiyarta, aka kuma rushe tushenta. 5Kush, Fut, da Lud, dukan Larabawa, Libiya, da mutanen ƙasar alkawari za su fāɗi tare da su ta takobi. 6Ga abin da Ubanmu ya ce, “Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi, ƙarfinta mai girman kai kuma zai sauka; daga Migdol zuwa Aswan za su fāɗi a cikinta ta takobi, in ji Maɗaukakin Uba. 7Za su zama kufai a cikin ƙasashe kufai, biranenta kuma za su kasance a cikin birane da suka rushe. 8Sa'an nan za su san cewa ni ne Uba, sa'ad da na sa wuta a Masar aka kuma ragargaza dukan masu taimakonta.
9A ranan nan manzanni za su fita daga wurina a cikin jiragen ruwa domin su razana Kush mai zaman lafiya, azaba kuma za ta kama su a ranar Masar—gama lalle tana zuwa.
10Ga abin da Maɗaukakin Uba ya ce, “Zan kawo ƙarshen taron jama'ar Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babila. 11Shi da mayaƙansa tare da shi, mafiya zalunci cikin al'ummai, za a kawo su domin su hallaka ƙasar; za su zāre takubansu a kan Masar su kuma cika ƙasar da matattu. 12Zan busar da rafukan Nilu in kuma sayar da ƙasar ga mugaye; zan mai da ƙasar kango, da kuma dukan abin da yake cikinta, ta hannun baƙi. Ni, Uba, na faɗa.”
13Ga abin da Maɗaukakin Uba ya ce, “Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofin banza a Memfis. Ba za a ƙara samun sarki a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro ko'ina a ƙasar. a a v13 Memfis babban birni ne na dā na Masar ta Ƙasa — a cikin Ibraniyancin Ezekiyel ana kiranta Nof. 14Zan mai da Fatros kango, in sa wuta a Zowan, in kuma zartar da hukunci a kan Tebes. b b v14 Tebes babban birni ne na Masar ta Bisa — a cikin Ibraniyancin Ezekiyel ana kiranta No. 15Zan zubar da hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse taron jama'ar Tebes. 16Zan sa wuta a Masar; Felusiyum za ta murɗe cikin azaba, za a farfashe Tebes, Memfis kuma za ta fuskanci abokan gāba da rana. 17Samarin Heliyofolis da Fi-beset za su fāɗi ta takobi, biranen kansu kuma za su tafi bauta. 18A Tafanhes rana za ta yi duhu sa'ad da na karya karkiyar Masar a can, ƙarfinta mai girman kai kuma zai ƙare a cikinta. Girgije zai rufe ta, 'ya'yan garuruwanta kuma za su tafi bauta. 19Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar. Sa'an nan za su san cewa ni ne Uba.”
Uba Ya Karya Hannun Fir'auna
20A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari, a rana ta bakwai, maganar Ubanmu ta zo mini:
21Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna sarkin Masar; ba a ɗaure shi domin warkarwa ba, ba a kuma sa masa katako ba, don yă sami ƙarfin da zai iya riƙe takobi. 22Saboda haka ga abin da Maɗaukakin Uba ya ce, “Ina gāba da Fir'auna sarkin Masar. Zan karya hannuwansa—mai ƙarfi da wanda ya karye—in kuma sa takobi yă fāɗi daga hannunsa. 23Zan watsar da Masarawa cikin al'ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe. 24Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir'auna, Fir'auna kuma zai yi nishi a gaban sarkin Babila kamar mai mutuwa. 25Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babila, amma hannuwan Fir'auna za su fāɗi. Sa'an nan za su san cewa ni ne Uba, sa'ad da na sa takobina a hannun sarkin Babila, ya kuma miƙa shi a kan ƙasar Masar. 26Zan watsar da Masarawa cikin al'ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe. Sa'an nan za su san cewa ni ne Uba.”