Kacici-kacicin Uba na Gaggafu Biyu
Ka-cici-ka-cici game da gaggafa biyu, da kan itacen al'ul, da kurangar inabin da aka dasa a wani wuri, wanda aka fassara shi da Zadakiya yana karya rantsuwar da ya yi wa Babila yana kuma neman dawakai daga Masar. Ba zai kuɓuta ba. Duk da haka Ubanmu ya ce zai dasa nasa toho mai laushi a dutsen Isra'ila.
17 1Maganar Ubanmu ta zo mini,
2“Ɗan Mutum, ka yi kacici-kacici, ka kuma yi wa gidan Isra'ila misali, 3ka kuma ce, Uba Mai Iko Dukka ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, mai dogayen gashi, da gashin fuka-fukai masu launuka iri-iri, ta zo Lebanon ta ɗauki ƙwanƙolin itacen al'ul. 4Ta tsinke ƙwanƙolin sabbin rassanta ta kai shi ƙasar kasuwanci; ta sa shi a birnin 'yan kasuwa. 5Sa'an nan ta ɗauki wani irin ƙasar ta shuka shi a ƙasa mai albarka; ta sa shi kusa da ruwaye masu yawa domin yă yi girma kamar itaciyar rafi. 6Sai ta tsira ta zama kuringar inabi marar tsawo, mai yaɗuwa, wadda rassanta suka juya wajen gaggafar, saiwoyinta kuma suka kasance ƙarƙashinta. Ta haka ta zama kuringar inabi, ta fid da rassa, ta kuma aiko toho. 7Amma akwai wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashin fuka-fukai masu yawa, sai wannan kuringar inabi ta juya saiwoyinta gare ta, ta kuma miƙa rassanta gare ta domin ta sha ruwa mai yawa daga gare ta fiye da gadon da aka shuka ta a ciki. 8An shuka ta a ƙasa mai kyau kusa da ruwaye masu yawa, domin ta yi rassa ta kuma ba da 'ya'ya ta zama kuringar inabi mai daraja.’
9Ka ce, Haka Uba Mai Iko Dukka ya ce, “Za ta yi albarka? Ba za a tumɓuke saiwoyinta ba, a kakkaɓe 'ya'yanta, har dukan sabbin ganyenta su yanƙwane? Ba a bukatar babban ƙarfi ko babban taro don a tumɓuke ta tun daga saiwoyinta. 10Ko da yake an shuka ta, za ta yi albarka? Ba za ta yanƙwane ƙaƙaf ba sa'ad da iskar gabas ta buge ta—ta yanƙwane a gadon da ta yi girma a kai?”
11Sai maganar Ubanmu ta zo mini,
12“Ka ce wa gidan masu tawaye, Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba? Ka gaya musu, Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya kama sarkinta da shugabanninta, ya kuma kai su Babila. 13Ya ɗauki ɗaya daga cikin zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi ƙarƙashin rantsuwa, ya kuma kwashe manyan mutanen ƙasar, 14domin mulkin yă ƙasƙanta, kada yă sāke tashi, sai dai ta wurin kiyaye alkawarinsa yă tsira. 15Amma Zedekiya ya yi wa sarkin Babila tawaye, ya aiki jakadu zuwa Masar don neman dawakai da runduna mai yawa. Zai yi nasara? Wanda ya yi haka zai kuɓuta? Zai iya karya alkawari ya kuma kuɓuta?’
16“Muddin ina raye, in ji Uba Mai Iko Dukka, zai mutu a Babila, inda sarkin da ya naɗa shi sarki yake zaune—wanda ya rena rantsuwarsa, ya kuma karya alkawarinsa. 17‘Fir'auna da rundunarsa mai ƙarfi da sojoji masu yawa ba za su taimake shi a yaƙi ba, sa'ad da aka gina tudun mamaya aka kuma gina katangun yaƙi don a halaka rayuka masu yawa. 18Ya rena rantsuwa, ya karya alkawari; ya riga ya ba da hannunsa, duk da haka ya yi dukan wannan—ba zai kuɓuta ba.’
19Saboda haka Uba Mai Iko Dukka ya ce, “Muddin ina raye, zan sauko wa kansa rantsuwata da ya rena, da alkawarina da ya karya. 20‘Zan yaɗa taruna a kansa; zai kama a tarkona. Zan kai shi Babila in yi masa shari'a a can saboda cin amanar da ya yi mini. 21Zaɓaɓɓun jarumawa cikin rundunarsa za su mutu da takobi, waɗanda suka ragu kuma a warwatsa su ga kowace iska. Sa'an nan za ku sani cewa ni, Ubanku, na yi magana.’
22Haka Uba Mai Iko Dukka ya ce, “Ni kaina zan ɗauki reshe daga ƙwanƙolin itacen al'ul mai tsawo in shuka shi. Daga sabbin rassansa na sama zan karya wani ɗanyen toho, ni kaina kuma zan shuka shi a kan wani dutse mai tsawo, maɗaukaki. a a v22 Inda mulkokin mutane suka kāsa, Ubanmu ya yi alkawari zai shuka wani ɗanyen toho nasa—Sarki mai zuwa daga zuriyar Dawuda, wanda ya cika a cikin Yesu, wanda yake girma yă zama mulkin da yake ba da inuwa ga dukan mutane. 23A kan tsaunin Isra'ila mai tsawo zan shuka shi, zai kuma fid da rassa yă ba da 'ya'ya yă zama itacen al'ul mai daraja. A ƙarƙashinsa kowane irin tsuntsu zai yi zama, yă yi sheƙa a inuwar rassansa. 24Dukan itatuwan jeji kuma za su sani cewa ni ne Uba, wanda yake saukar da dogon itace, yake kuma sa gajeren itace yă yi tsawo, wanda yake busar da ɗanyen itace, yake kuma sa busasshen itace yă yi girma. Ni, Uba, na yi magana, zan kuma aikata shi.”