An Girmama Esta da Mordekai
Aka ba Esta gidan Haman, aka kuma ba Mordekai zoben hatiminsa, amma ba za a iya soke dokar kisan ba. Saboda haka doka ta biyu ta fita a kan dawakan sarki: Yahudawa za su iya taruwa su kāre rayukansu. Mordekai ya fita da tufafin sarauta shuɗi da zinariya, Shushan kuwa ta yi sowa.
8 1A ranan nan Sarki Zerzes ya ba Sarauniya Esta mallakar Haman, maƙiyin Yahudawa. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, domin Esta ta bayyana masa dangantakarta da shi. 2Sai sarki ya cire zoben hatiminsa, wanda ya karɓe daga Haman, ya ba Mordekai. Esta kuwa ta naɗa Mordekai a kan mallakar Haman.
3Esta ta sāke yi wa sarki magana, ta faɗi a ƙafafunsa, ta yi kuka, ta kuma roƙe shi yă dakatar da muguntar Haman mutumin Agag, da makircin da ya ƙulla a kan Yahudawa. 4Sarki kuwa ya miƙa wa Esta sandar sarauta ta zinariya, sai ta tashi ta tsaya a gabansa. 5Ta ce, “Idan ya gamshi sarki, in kuma na sami tagomashinsa, in wannan ya yi daidai a gare shi, in kuma na gamshe shi, to, a rubuta wasiƙu domin a soke abin da Haman ɗan Hammedata mutumin Agag ya ƙulla ya kuma rubuta don a hallaka Yahudawa a cikin dukan larduna na sarki. 6Yaya zan iya jure ganin masifa ta auko wa mutanena? Yaya kuma zan iya jure ganin an hallaka iyalina?”
7Sarki Zerzes ya ce wa Sarauniya Esta da Mordekai Bayahude, “Na ba Esta gidan Haman, su kuma suka rataye shi a kan gungume domin ya ƙulla makirci a kan Yahudawa. 8Ku rubuta game da Yahudawa yadda kuka ga ya dace, da sunan sarki, ku kuma hatimce shi da zoben hatiminsa, gama rubutun da aka yi da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa, ba a iya sokewa ba.”
9Sai aka kira marubutan sarki a rana ta ashirin da uku ga wata na uku, wato watan Sifan, suka kuma rubuta dukan abin da Mordekai ya umarta ga Yahudawa, da ga manyan shugabanni, da gwamnoni, da hafsoshi na larduna ɗari da ashirin da bakwai, daga Indiya har zuwa Kush: kowane lardi da rubutunsa, kowane mutane da harshensu, Yahudawa kuma da rubutunsu da harshensu. 10Mordekai ya rubuta da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce shi da zoben hatimin sarki, ya kuma aika wasiƙun ta hannun manzanni a kan dawakai masu sauri da aka yi kiwonsu domin hidimar sarauta. 11Dokar sarki ta ba Yahudawa da suke cikin kowane birni izini su taru su kuma kāre rayukansu: wato su hallaka, su kashe, su kuma kawar da duk wani runduna mai ɗauke da makamai na kowane mutane ko lardi da ya kai musu hari, har da yara da mata, su kuma washe dukiyar maƙiyansu. 12Wannan zai faru a rana ɗaya a cikin dukan larduna na Sarki Zerzes, wato a rana ta goma sha uku ga wata na goma sha biyu, wato watan Adar. 13Za a fitar da kwafin dokar a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da ita ga dukan mutane, domin Yahudawa su kasance a shirye a ranan nan su rama wa kansu a kan maƙiyansu. 14Manzannin da suke kan dawakan sarauta suka ruga da sauri, da gaggawa bisa umarnin sarki; aka kuma ba da dokar a cikin fadar Shusha.
15Mordekai ya fito daga gaban sarki sanye da tufafin sarauta masu launin shuɗi da fari, da babban kambi na zinariya, da kuma riga ta lallausan lilin mai launin shunayya. Birnin Shusha kuwa ya yi sowa ya kuma yi murna. 16Yahudawa kuwa suka sami haske, da farin ciki, da murna, da girma. 17A kowane lardi da birni da umarnin sarki da dokarsa suka kai, sai Yahudawa suka yi farin ciki da murna, da buki, da hutun idi. Mutane da yawa na ƙasar kuwa suka zama Yahudawa, gama tsoron Yahudawa ya kama su.