Yanzu a bugun takarda

2 Tasalonikawa 3 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ku Yi Addu'a Domin Magana Ta Yaɗu Cikin 'Yanci

Bulus ya roƙi addu'a domin maganar ta yi gaba, sa'an nan ya juya ga wata matsala: waɗansu a cikin ikkilisiya sun daina aiki sun zama masu shisshigi, suna rayuwa a kan wasu. Ya nuna aikinsa na dare da rana. Ku lura da irin wannan mutum, kada ku yi cuɗanya da shi, amma ku gargaɗe shi kamar ɗan'uwa, ba kamar maƙiyi ba.

Babi na 3.

A ƙarshe, 'yan'uwa, ku yi mana addu'a domin maganar Ubangijinmu Yesu ta yaɗu da sauri ta kuma sami girmamawa, kamar yadda ta kasance a cikinku, a kuma cece mu daga mugaye da karkatattun mutane; gama ba kowa ne mai bi ba. Amma Ubangiji mai aminci ne, wanda zai ƙarfafa ku ya kuma tsare ku daga mugun nan. Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna yi, za ku kuma ci gaba da yin, abin da muka umarce ku. Bari Ubangiji yă bi da zukatanku cikin ƙaunar Ubanmu da kuma cikin haƙurin Almasihu.

Gargaɗi A Kan Ragwanci

'Yan'uwa, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu muka umarce ku, ku nisanci kowane ɗan'uwa da yake zaman ragwanci, wanda ya saɓa wa al'adar da kuka karɓa daga gare mu. Ku kanku kun san ya kamata ku yi koyi da mu, gama ba mu yi zaman ragwanci a cikinku ba. Ba mu ci abincin kowa a banza ba; a maimakon haka muka yi aiki dare da rana, cikin wahala da ƙunci, domin kada mu zama wa waninku nauyi. Ba don ba mu da hakkin yin haka ba ne, sai dai domin mu mayar da kanmu abin koyi a gare ku, ku bi. Har ma sa'ad da muke tare da ku, muka umarce ku cewa, in wani ya ƙi yin aiki, kada yă ci abinci. Gama mun ji cewa waɗansu a cikinku suna zaman ragwanci, ba sa aiki sai dai suna shisshigin al'amuran waɗansu. Muna umarni muna kuma gargaɗin irin waɗannan mutane cikin Ubangiji Yesu Almasihu, su yi aiki a hankali, su ci abincinsu. Amma ku, 'yan'uwa, kada ku gaji da yin nagarta. In wani ya ƙi yin biyayya ga maganarmu da ke cikin wannan wasiƙa, ku lura da shi, kada kuma ku yi cuɗanya da shi, domin yă ji kunya. Amma kada ku ɗauke shi maƙiyi, sai dai ku gargaɗe shi kamar ɗan'uwa.

Salama, Gaisuwa, da Alheri

Bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama kullum, ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.

Ni, Bulus, na rubuta wannan gaisuwa da hannuna—alama ce da take tabbatar da cewa kowace wasiƙa daga gare ni ta gaskiya ce; haka nake rubutu. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă kasance tare da ku duka.