Rabbah Ta Faɗi, Dawuda Kuma Ya Sa Rawani
Yowab ne ke yaƙi a Rabba yayin da Dawuda ya zauna a gida, ko da yake a nan sarkin ya iso ya karɓi kambin. Sa'an nan faɗace-faɗace uku da ƙattan Filistiyawa, har da wani mutum mai yatsu shida wanda ya yi wa Isra'ila ba'a, ɗan wan Dawuda kuma ya kashe shi.
20 1Da shekara ta kewayo, lokacin da sarakuna sukan fita yaƙi, sai Yowab ya fitar da rundunar yaƙi ya kuma lalatar da ƙasar Ammonawa, sa'an nan ya zo ya kewaye Rabbah, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabbah ya rushe ta. 2Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu. Nauyinsa ya kai kusan fam saba'in da biyar na zinariya, an kuma sa masa dutse mai daraja, aka sa shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga birnin. 3Ya fitar da mutanenta ya sa su yin aiki da zartuka, da sumul na ƙarfe, da gatura. Dawuda ya yi haka ga dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan rundunarsa suka koma Urushalima.
Kattai Suka Faɗi a Hannun Isra'ila
4Bayan wannan, sai yaƙi ya ɓarke da Filistiyawa a Gezer. A lokacin nan sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Sippai, ɗaya daga cikin zuriyar Rafa, aka kuma rinjayi Filistiyawa.
5Yaƙi ya sāke ɓarkewa da Filistiyawa. Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi, ɗan'uwan Goliyat mutumin Gat, wanda ƙotar māshinsa ta yi kauri kamar babban katako mai nauyi. 6Har wa yau sai yaƙi ya ɓarke a Gat, inda akwai wani mutum kato, yana da yatsotsi shida a kowane hannu da yatsotsi shida a kowace ƙafa, ashirin da huɗu duka—shi ma an haife shi ga Rafa. 7Da ya zagi Isra'ila, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan'uwan Dawuda, ya buge shi ya kashe. 8Waɗannan an haife su ne ga Rafa a Gat, suka kuma faɗi a hannun Dawuda da bayinsa.