Isra'ila Sun Ƙudiri Neman Ubanmu
Dawuda ya nemi shawarar kowa ya kuma kwashe akwatin Ubanmu da aka yi watsi da shi a kan sabon keken shanu. Sa'ad da shanun suka yi tuntuɓe Uzza ya riƙe shi, sai ya mutu nan take. Dawuda ya yi fushi, sa'an nan tsoro, aka ajiye akwatin a gidan Obed-edom — inda aka albarkaci iyalin.
13 1Dawuda ya tattauna da shugabannin dubbai da na ɗarurruwa, da kowane shugaba. 2Dawuda ya ce wa dukan taron Isra'ila, “In kuka ga ya yi kyau, in kuma daga wurin Ubanmu ne, bari mu aika saƙo ko'ina zuwa ga sauran 'yan'uwanmu da suke a dukan ƙasashen Isra'ila, tare da su firistoci da Lawiyawa da suke a cikin biranensu da wuraren kiwonsu, su taru wurinmu. 3Bari mu dawo da akwatin alkawarin Ubanmu wurinmu, gama ba mu neme shi ba a zamanin Shawulu.”
4Dukan taron kuwa suka yarda su yi haka, gama abin ya yi daidai a gaban dukan jama'a.
5Sai Dawuda ya tara dukan Isra'ila daga Shihor na Masar har zuwa Lebo-hamat, domin su dawo da akwatin alkawarin Ubanmu daga Kiriyat-yeyarim.
6Dawuda da dukan Isra'ila suka haura zuwa Ba'ala, wato Kiriyat-yeyarim da yake a Yahuda, domin su kawo daga can akwatin alkawarin Ubanmu, wanda yake zaune bisa kerubobi, inda ake kiran sunansa. 7Suka ɗauki akwatin alkawarin Ubanmu a kan sabuwar keken shanu daga gidan Abinadab; Uzza da Ahiyo ne suka bi da keken. 8Dawuda da dukan Isra'ila kuwa suka yi farin ciki a gaban Ubanmu da dukan ƙarfinsu, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da gangunan hannu, da kuge, da ƙahoni.
9Da suka iso masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa domin yă kama akwatin, gama shanu suka yi tuntuɓe. 10Sai fushin Ubanmu ya ƙuna a kan Uzza, ya kuma buge shi saboda ya miƙa hannunsa ga akwatin; ya kuwa mutu a can a gaban Ubanmu. 11Dawuda ya yi fushi domin Ubanmu ya auka wa Uzza, saboda haka ake kiran wurin nan Ferez-uzza har wa yau. 12Dawuda ya ji tsoron Ubanmu a ranar, yana cewa, “Yaya zan iya kawo akwatin alkawarin Ubanmu wurina?” 13Saboda haka Dawuda bai kawo akwatin zuwa birnin Dawuda ba; sai ya karkata da shi zuwa gidan Obed-edom Bagitti. 14Akwatin alkawarin Ubanmu ya zauna tare da iyalin Obed-edom a gidansa wata uku, Ubanmu kuma ya albarkaci iyalin Obed-edom da dukan abin da yake da shi.