Ma'aunin Gaskiya Shi Ne Farin Cikinsa
Ma'aunai, karimci da suna su ne suka fi yawa. Babin yana ta nanata cewa abin da yake kama da hasara ba hasara ba ne: mutum ya bayar hannu sake ya ƙara arziki, ya ɓoye hatsi a la'ance shi saboda haka. Kyau marar hankali ya sami kalma mafi kaifi: zoben zinariya a hancin alade.
11 1Ma'aunin ha'inci abin ƙyama ne ga Ubanmu, amma ma'aunin gaskiya shi ne farin cikinsa. 2Sa'ad da girman kai ya zo, sai kunya ta biyo, amma hikima tana tare da masu tawali'u. 3Amincin masu adalci yakan shiryar da su, amma karkatar mayaudara takan hallaka su. 4Dukiya ba ta amfana a ranar fushi ba, amma adalci yakan ceto daga mutuwa. 5Adalcin marar aibi yakan miƙe masa hanya, amma mugu yakan faɗi ta dalilin muguntarsa. 6Adalcin masu gaskiya yakan ceto su, amma ana kama mayaudara a tarkon kwaɗayinsu. 7Sa'ad da mugu ya mutu, begensa yakan ƙare, dogaronsa kuma ga ƙarfinsa yakan zama banza. 8An ceci mai adalci daga wahala, mugu kuma yakan shiga cikinta a maimakonsa. 9Da bakinsa marar tsoron Allah yakan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani akan ceci masu adalci. 10Sa'ad da masu adalci suke cikin wadata, birni yakan yi murna, kuma sa'ad da mugaye suka hallaka, akan yi ihun murna. 11Ta wurin albarkar masu gaskiya ake ɗaukaka birni, amma ta bakin mugaye ake rushe shi. 12Wanda yake rena maƙwabcinsa marar hankali ne, amma mai ganewa yakan yi shiru. 13Mai gulma yakan yi ta yawo yana tona asirai, amma mai amintaccen ruhu yakan kiyaye asiri. 14Inda babu ja-gora, al'umma takan fāɗi, amma cikin yawan mashawarta akwai tsira. 15Wanda ya ba da lamuni domin baƙo lalle zai sha wahala, amma wanda yake ƙin yin alkawari da shan hannu yana cikin aminci. 16Mace mai alheri takan sami girmamawa, maza marasa tausayi kuma sukan sami dukiya. 17Mai kirki yakan amfani kansa, amma mutum mai zalunci yakan kawo wa kansa wahala. 18Mugu yakan sami albashi na ruɗu, amma wanda yake shuka adalci yakan sami lada ta gaskiya. 19Wanda yake tsaye daram cikin adalci yakan sami rai, amma wanda yake bin mugunta gudu yake yi zuwa mutuwarsa. 20Masu karkataccar zuciya abin ƙyama ne ga Ubanmu, amma waɗanda hanyoyinsu babu aibi su ne farin cikinsa. 21Ka tabbata mugu ba zai rasa hukunci ba, amma 'ya'yan masu adalci za su kuɓuta. 22Kamar zoben zinariya a hancin alade haka mace kyakkyawa wadda ba ta da basira take. 23Sha'awar masu adalci takan ƙare da alheri kaɗai, amma begen mugaye yakan ƙare da fushi. 24Wani yakan yi bayarwa hannu sake, duk da haka yakan ƙara wadata; wani kuma yakan hana abin da ya dace, sai ya ƙarasa cikin bukata. 25Mai karimci za a wadatar da shi, kuma wanda yake wartsake waɗansu shi kansa za a wartsake shi. 26Jama'a sukan la'anci wanda yake hana hatsi, amma wanda yake sayar da shi yana da albarka. 27Wanda yake himma ga neman alheri, yana neman tagomashi ne, amma wanda yake neman mugunta, mugunta za ta same shi. 28Wanda yake dogara ga dukiyarsa zai faɗi, amma masu adalci za su yi fure kamar koren ganye. 29Wanda yake kawo wahala a gidansa zai gāji iska, wawa kuma zai zama bawa ga mai hikima a zuci. 30'Ya'yan masu adalci itacen rai ne, wanda kuma yake jawo rayuka mai hikima ne. 31Idan ana sāka wa mai adalci a duniya, balle fa mugu da mai zunubi!