Ka Ta'azantar da Ni
Gajeriyar waƙa domin ranar da ke bayan hukunci. Mawaƙin ya gode wa Ubansa a fili saboda fushin da ya kau da ta'aziyyar da ta zo, ya kuma ce zai dogara ba zai ji tsoro ba. Ana ɗebo ruwa da farin ciki, Sihiyona kuma tana raira waƙa domin Mai Tsarki yana kusa.
12 1A ranan nan za ka ce, “Zan yabe ka, ya Ubana, gama ko da yake ka yi fushi da ni, fushinka ya huce, ka kuma ta'azantar da ni. 2Ga shi, Ubanmu shi ne cetona; zan dogara, ba kuwa zan ji tsoro ba, gama Ubana shi ne ƙarfina da waƙata; ya zama cetona.” 3Da farin ciki za ka ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto. 4A ranan nan za ka ce, “Ku gode wa Ubanmu, ku kira bisa sunansa, ku yi shelar ayyukansa ga dukan mutane, ku yi shela cewa an ɗaukaka sunansa. 5Ku rera wa Ubanmu, gama ya aikata abubuwa masu ɗaukaka; bari a san wannan a dukan duniya. 6Ka yi sowa da ƙarfi ka kuma rera don murna, ya mazaunin Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra'ila—Ubanmu—mai girma ne a cikinka.”