Sāke Gina Gidan Ubanmu
Haggai da Zakariya suka motsa Zarubabel da Yeshuwa, suka sake fara gini. Gwamna Tattenai ya nemi sanin wa ya ba su izini, amma idon Ubansu yana kan dattawan, don haka ba wanda ya tsai da su. Rahoton Tattenai zuwa ga Dariyus ya roƙa kawai a bincika ajiyar takardun sarauta.
5 1Sai annabawa Haggai da Zakariya ɗan Iddo suka yi annabci ga Yahudawan da suke a Yahuda da Urushalima, da sunan Ubanmu, Allah na Isra'ila, wanda yake bisa kansu. 2Sai Zerubabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka tashi suka fara sāke gina gidan Ubanmu a Urushalima, annabawan Ubanmu kuwa suna tare da su, suna goyon bayansu.
3Sai Tattenai, gwamnan Hayin-Kogi, da Shetar-bozenai, da abokan aikinsu suka zo suka tambaya, “Wa ya ba ku izini ku gina wannan gida ku kuma gama wannan ginin?” 4Suka kuma tambaya, “Mene ne sunayen mutanen da suke gina wannan ginin?” 5Amma idon Ubansu yana kan dattawan Yahudawa, saboda haka ba wanda ya hana su sai da maganar ta kai ga Dariyus, aka kuma mayar da amsa a rubuce.
Wasiƙa zuwa ga Sarki Dariyus
6Ga kwafin wasiƙar da Tattenai, gwamnan Hayin-Kogi, da Shetar-bozenai tare da abokan aikinsa shugabanni na Hayin-Kogi, suka aika wa Sarki Dariyus. 7Suka aika masa rahoto mai cewa, Zuwa ga Sarki Dariyus, cikakkiyar salama.
8Sarki, ka sani, mun tafi lardin Yahuda, zuwa gidan Allah mai girma. Ana gina shi da manyan duwatsu, ana kuma kafa katako a cikin bangwaye. Aikin yana ci gaba da himma yana kuma bunƙasa a hannunsu. 9Saboda haka muka tambayi dattawan, “Wa ya ba ku izini ku gina wannan gida ku kuma gama wannan ginin?” 10Muka kuma tambayi sunayensu, domin mu sanar da kai, domin kuma mu rubuta sunayen shugabanninsu. 11Suka amsa mana suka ce, “Mu bayin Ubanmu ne, Allah na sama da ƙasa, muna kuma sāke gina gidan da wani babban sarkin Isra'ila ya gina ya kuma gama shekaru masu yawa da suka wuce. 12Amma domin kakanninmu sun fusata Ubanmu, Allah na sama, sai ya ba da su ga Nebukadnezzar na Babila, sarkin Babila, wanda ya rushe wannan gida ya kuma kori mutanen zuwa zaman bauta a Babila. 13Amma a shekara ta farko ta Sairus sarkin Babila, Sairus sarki ya ba da umarni a sāke gina wannan gidan Ubanmu. 14Sairus sarki ya kuma fito da kayan zinariya da na azurfa na gidan Ubanmu daga haikalin Babila, waɗanda Nebukadnezzar ya ɗauko daga haikalin da yake a Urushalima ya kai su haikalin Babila. Ya ba da su ga wani mai suna Sheshbazzar, wanda ya naɗa shi gwamna, 15yana ce masa, ‘Ka ɗauki waɗannan kaya, ka je ka ajiye su a haikalin Urushalima, bari kuma a sāke gina gidan Allah a wurinsa.’ 16Sai wannan Sheshbazzar ya zo ya kafa harsashin gidan Ubanmu a Urushalima; tun daga lokacin har yanzu ana ta ginawa, amma har yanzu ba a gama ba.”
17To, in sarki ya yarda, bari a yi bincike a cikin ma'ajin takardun sarauta a Babila, don a ga ko Sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina wannan gidan Allah da yake a Urushalima. Sa'an nan bari sarki ya aiko mana da shawararsa a kan wannan magana.