Ba Mai Tsira daga Hannun Uba
Babu inda za a ɓuya daga Ubanmu — ba kabari ba, ba sama ba, ba ƙasan teku ba. Duk da haka girgizar rariya ce, ba ko tsakuwa ɗaya da za ta faɗi. Kalma ta ƙarshe sake ginawa ce: za a tayar da rumfar Dawuda da ta faɗi, a zauna a biranen da suka lalace, a dasa Isra'ila kuma ba za a ƙara tumɓuke ta ba.
9 1Na ga Uba Mai Iko Duka yana tsaye kusa da bagade, sai ya ce, “Ka buge kan ginshiƙai har madogarai su girgiza, ka kuma farfasa su a kan dukansu; sauran kuma zan kashe su da takobi. Ba wanda zai gudu, ba wanda zai tsira. 2Ko sun tona har zuwa kabari, daga can hannuna zai kama su; ko sun hau zuwa sama, daga can zan sauko da su. 3Ko sun ɓoye kansu a kan dutsen Karmel, daga can zan neme su in kama su; ko sun ɓuya daga gabana a ƙarƙashin teku, can zan umarci maciji, zai kuwa cije su. 4Ko sun tafi bauta a gaban abokan gābansu, can zan umarci takobi, zai kuwa kashe su; zan kafa idanuna a kansu domin cuta ba domin alheri ba.”
5Uba Mai Iko Duka, Uban rundunonin sama — shi da yake taɓa ƙasa ta kuwa narke, duk masu zama a cikinta kuwa su yi makoki; dukanta ta kumbura kamar Nilu ta kuma nutse kamar Nilu na Masar, 6Shi da yake gina ɗakunansa na sama a sammai ya kuma kafa rufinsa a bisa ƙasa, shi da yake kiran ruwayen teku ya kuma zuba su a bisa fuskar ƙasa — Ubanmu ne sunansa.
7“Ba kamar 'ya'yan Kushawa kuke a gare ni ba, ya ku 'ya'yan Isra'ila?” In ji Ubanmu. “Ba ni ne na fito da Isra'ila daga ƙasar Masar ba, da Filistiyawa daga Kaftor da Arameyawa daga Kir ba? 8Ga shi, idanun Uba Mai Iko Duka suna a kan mulkin mai zunubi, zan kuwa hallaka shi daga fuskar ƙasa — amma ba zan hallaka gidan Yakubu ƙaƙaf ba,” in ji Ubanmu. 9“Gama ga shi, zan ba da umarni, zan kuwa jijjiga gidan Isra'ila cikin dukan al'ummai kamar yadda akan tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi, amma ko tsakuwa ɗaya ba za ta fāɗi ƙasa ba. 10Dukan masu zunubi na cikin mutanena za su mutu da takobi — waɗanda suke cewa, ‘Masifa ba za ta same mu ko ta cim mana ba.’”
Uba Zai Maido da Mutanensa
11“A ranar nan zan tā da bukkar Dawuda da ta fāɗi, in gyara ɓaraka-ɓarakanta, in tā da kufansa, in sāke gina ta kamar a kwanakin dā, 12domin su mallaki raguwar Edom da dukan al'umman da ake kira da sunana,” in ji Ubanmu, wanda yake yin wannan.
13“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubanmu, “sa'ad da mai noma zai cim ma mai girbi, mai matsin inabi kuma zai cim ma mai shuka iri; duwatsu za su ɗiga ruwan inabi mai zaƙi, dukan tuddai kuma za su yi gudu da shi. a a v13 Hoton shi ne: girbi zai yi yawa ƙwarai har girbin hatsi ya yi tarayya da shukar da ta biyo baya, matsin inabi kuma ya ci gaba har zuwa lokacin shuka — abin al'ajabi na yalwa marar misaltuwa. 14Zan mai da arzikin mutanena Isra'ila, za su kuwa sāke gina biranen da suka rushe su zauna a cikinsu; za su shuka gonakin inabi su sha ruwansa, su yi lambuna su ci 'ya'yansu. 15Zan dasa su a ƙasarsu, ba kuwa za a ƙara tumɓuke su ba daga ƙasar da na ba su,” in ji Ubanku.