An Daure Dodon Ruwa
An ɗaure Shaiɗan da sarƙa shekara dubu, yayin da shahidan da suka ƙi dabbar suke mulki. Da aka sake shi, ya tara al'ummai sau na ƙarshe, wuta daga wurin Ubanmu kuwa ta cinye su. Sa'an nan aka buɗe littattafai, aka yi wa matattu shari'a bisa ga abin da suka aikata. Mutuwa kanta aka jefar da ita.
20 1Sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, yana riƙe da mabuɗin lungun ƙasa da kuma babbar sarƙa a hannunsa. 2Sai ya kama dodon, wato tsohon macijin nan, wato Iblis da Shaiɗan, ya daure shi shekara dubu. 3Sai ya jefa shi cikin lungun ƙasa, ya rufe, ya kuma sa hatimi a kansa, domin kada yă ƙara ruɗin al'ummai sai shekara dubun nan ta cika. Bayan haka, dole a sake shi na ɗan lokaci kaɗan.
4Sai na ga kursiyoyi, waɗanda kuma suka zauna a kansu suka sami ikon yin shari'a. Na kuma ga rayukan waɗanda aka fille musu kai saboda shaidarsu game da Yesu da kuma maganar Ubanmu—waɗanda ba su bauta wa dabbar nan ba, ko siffarta, ba su kuma karɓi alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba. Suka rayu, suka kuma yi mulki tare da Almasihu shekara dubu. 5(Sauran matattu kuwa ba su rayu ba sai shekara dubun nan ta cika.) Wannan shi ne tashin matattu na farko. 6Mai albarka ne, mai tsarki kuma, duk wanda yake da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, amma za su zama firistocin Ubanmu da na Almasihu, za su kuma yi mulki tare da shi shekara dubu.
An Saki Shaiɗan
7Sa'ad da shekara dubun nan ta cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukunsa. 8Zai fita don yă ruɗi al'ummai a kusurwoyi huɗu na duniya—wato Gog da Magog—yă tara su don yaƙi, yawansu kuwa kamar yashin bakin teku. a a v8 Gog da Magog ba al'ummai biyu ne na ainihi ba, sai dai alamu ne, waɗanda aka ciro daga littafin annabi Ezekiyel, suna misalta dukan mutanen duniya masu tawaye waɗanda suka taru gāba da mutanen Ubanmu. 9Suka bazu ko'ina a faɗin duniya, suka kewaye sansanin tsarkaka da kuma birni ƙaunatacce, amma sai wuta ta sauko daga wurin Ubanmu daga Sama, ta cinye su. 10Aka jefa Iblis wanda ya ruɗe su cikin tafkin wuta da farar wuta mai ci, inda dabbar nan take da annabin ƙarya. Za a wahalshe su dare da rana har abada abadin.
Babban Farin Kursiyi
11Sai na ga wani babban farin kursiyi da wanda yake zaune a kansa. Duniya da Sama suka gudu daga gabansa, babu kuma wurin da ya rage musu. b b v11 Babban farin kursiyin shari'a ta ƙarshe, kursiyin Ubanmu ne. Kowane mutum da ya taɓa rayuwa yana tsaye a gabansa. 12Na kuma ga matattu, manya da ƙanana, suna tsaye a gaban kursiyin. Sai aka buɗe littattafai, aka kuma buɗe wani littafi dabam—wato littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake rubuce a cikin littattafan, kowanne bisa ga ayyukansa. 13Teku ya ba da matattunsa, Mutuwa da kabari kuma suka ba da nasu, aka yi wa kowanne shari'a bisa ga abin da ya aikata. 14Sai aka jefa Mutuwa da kabari cikin tafkin wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu—wato tafkin wuta. 15Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a littafin rai ba, sai aka jefa shi cikin tafkin wuta.