Ubanmu ya Naɗa Yoshuwa
Cin nasara da zaunar da Ƙasar Alkawari a ƙarƙashin Yoshuwa. Yayin da wani aiki mai ban tsoro ke farawa, Ubanmu ya kafa jama'arsa ba a kan ƙarfin zuciyarsu ba, sai dai a kan kasancewarsa tare da su.
1 1Bayan mutuwar Musa bawan Ubanmu, sai Ubanmu ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,
2“Musa bawana ya mutu. Yanzu ka tashi, ka ƙetare Urdun, kai da dukan mutanen nan, zuwa ƙasar da nake ba su, 'ya'yan Isra'ila. 3Kowane wuri da ƙafarka ta taka na ba ka shi, yadda na yi alkawari wa Musa. 4Iyakar ƙasarka za ta tashi daga jeji da Lebanon nan har zuwa babban kogin Yuferatis — dukan ƙasar Hittiyawa — har zuwa Babban Teku wajen faɗuwar rana. 5Babu wanda zai iya tsayawa gabanka dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan rabu da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.
6“Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi ƙarfin zuciya, gama kai ne za ka sa mutanen nan su gāji ƙasar da na rantse wa kakanninsu zan ba su. 7Sai dai ka yi ƙarfin hali ƙwarai da gaske, ka yi hankali ka kiyaye dukan shari'ar da Musa bawana ya umarce ka. Kada ka kauce mata dama ko hagu, domin ka yi nasara duk inda ka tafi. 8Kada ka bari Littafin Shari'a nan ya rabu da bakinka; ka yi ta tunaninsa dare da rana, domin ka kiyaye ka aikata dukan abin da aka rubuta a cikinsa. Sa'an nan hanyarka za ta yi arziki, kai kuma za ka yi nasara. 9Ashe, ban umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali, ka yi ƙarfin zuciya. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai, gama ni, Ubanka, ina tare da kai duk inda ka tafi.”
Yoshuwa ya Tattara Mutane su Ƙetare
10Sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane,
11“Ku ratsa sansani, ku umarci mutane, ‘Ku shirya guzuri, gama bayan kwana uku za ku ƙetare Urdun domin ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubanku yake ba ku ku mallaka.’”
12Amma ga mutanen Ra'ubainu, da mutanen Gad, da rabin kabilar Manassa, Yoshuwa ya ce,
13“Ku tuna da abin da Musa bawan Ubanmu ya umarce ku, ‘Ubanku yana ba ku hutu, zai kuma ba ku ƙasar nan.’ 14Matanku, da 'ya'yanku, da dabbobinku za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun; amma dukanku jarumawa za ku ƙetare da makamai gaban 'yan'uwanku domin ku taimake su, 15har sai Ubanmu ya ba 'yan'uwanku hutu kamar yadda ya ba ku, su kuma su mallaki ƙasar da yake ba su. Sa'an nan ku komo ƙasarku ku mallake ta — ƙasar da Musa bawan Ubanmu ya ba ku a gaba da Urdun wajen fitowar rana.”
16Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Dukan abin da ka umarce mu za mu yi, kuma duk inda ka aike mu za mu tafi. 17Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya cikin kome, haka za mu yi maka biyayya. Sai dai Ubanka yă kasance tare da kai, kamar yadda ya kasance tare da Musa. 18Duk wanda ya yi tawaye ga umarninka, ya ƙi yin biyayya ga maganarka cikin duk abin da ka umarta, dole a kashe shi. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi ƙarfin zuciya.”