Ba Karusai Ba, Sai Sunansa
Don mai bi da waƙa. Zabura ta Dawuda.
Taron jama'a suna yi wa sarki addu'a kafin ya fita yaƙi: Allah ya tuna da hadayunka, ya cika shirye-shiryenka, ya amsa roƙe-roƙenka. Juyawar tana zuwa a tsakiya — waɗansu suna dogara ga karusai da dawakai, amma waɗannan mutane suna dogara ga sunan Ubanmu.
20 1Bari Ubanmu yă amsa maka a ranar wahala; bari sunan Allahn Yaƙubu yă kāre ka. 2Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki, yă kuma riƙe ka daga Sihiyona. 3Bari yă tuna da dukan hadayunka, yă kuma yarda da hadayarka ta ƙonawa. 4Bari yă ba ka begen zuciyarka, yă kuma cika dukan shirye-shiryenka.
5Za mu yi sowa ta murna saboda cetonka, za mu kuma daga tutocinmu da sunan Ubanmu. Bari Ubanmu yă cika dukan roƙe-roƙenka. 6Yanzu na sani cewa Ubanmu yana ceton shafaffensa; yana amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannunsa na dama. 7Waɗansu suna dogara ga karusai, waɗansu kuma ga dawakai, amma mu, muna dogara ga sunan Ubanmu. 8Su, sun durƙusa suka fāɗi, amma mu, mun tashi muka tsaya daram. 9Ya Ubanmu, ka ceci sarki! Ka amsa mana sa'ad da muke kira.