'Ya'ya Matan Zelofehad
'Yan'uwa mata biyar suka tambaya don me sunan mahaifinsu zai ɓace domin rashin ɗa, Ubanmu kuma ya ce gaskiya suke faɗa, ya canja dokar gādo. Musa, da aka faɗa masa zai mutu a bayan ƙasar, ya roƙi makiyayi domin mutanen; aka naɗa Yoshuwa a gaban dukansu.
27 1'Ya'ya mata na Zelofehad ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, daga kabilan Manassa ɗan Yusufu, suka matso kusa. Sunayen 'ya'yansa mata su ne: Mala, Nowa, Hogla, Milka, da Tirza. 2Suka tsaya a gaban Musa, da Ele'azara firist, da shugabanni, da dukan jama'a, a ƙofar Tentin Sujada, suka ce, 3“Mahaifinmu ya mutu a jeji. Bai kasance cikin waɗanda suka taru gāba da Ubanmu tare da ƙungiyar Kora ba; ya mutu saboda zunubin kansa, kuma ba shi da 'ya'ya maza. 4Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace daga kabilarsa domin ba shi da ɗa? Ka ba mu mallaka a cikin 'yan'uwan mahaifinmu.”
5Sai Musa ya kawo ƙararsu a gaban Ubanmu. 6Ubanmu ya ce wa Musa,
7“'Ya'ya matan Zelofehad gaskiya suke faɗa. Ka ba su rabon gādo a cikin 'yan'uwan mahaifinsu, ka kuma mai da gādon mahaifinsu zuwa gare su. 8Ka gaya wa Isra'ilawa cewa, in mutum ya mutu babu ɗa, za ku mai da gādonsa ga 'yarsa. 9In ba shi da 'ya mace, sai ku ba da gādonsa ga 'yan'uwansa. 10In ba shi da 'yan'uwa, sai ku ba da gādonsa ga 'yan'uwan mahaifinsa. 11In mahaifinsa ba shi da 'yan'uwa, sai ku ba da gādonsa ga danginsa na kusa a cikin kabilarsa, shi kuma zai mallake shi. Wannan za tă zama farillar shari'a ga Isra'ilawa, yadda Ubanmu ya umarci Musa.”
Musa Ya Ga Ƙasar
12Sa'an nan Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka hau Dutsen Abarim ka ga ƙasar da na ba Isra'ilawa. 13Sa'ad da ka gan ta, kai ma za a tara ka ga mutanenka, yadda aka tara Haruna ɗan'uwanka, 14domin kun yi tawaye ga umarnina a jejin Zin, a lokacin faɗar jama'a, sa'ad da ya kamata ku tsarkake ni a gaban idanunsu wajen ruwa—wato ruwan Meriba na Kadesh, na jejin Zin.”
15Musa ya yi magana da Ubanmu, yana cewa, 16“Bari Uban ruhohin dukan nama yă naɗa mutum a kan jama'a, 17wanda zai fita a gabansu yă kuma shiga a gabansu, wanda zai fitar da su yă kuma shigar da su, domin kada jama'ar Ubanmu su zama kamar tumaki marasa makiyayi.”
18Sai Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka ɗauki Yoshuwa ɗan Nun, mutum mai Ruhun Ubanmu a cikinsa, ka ɗora hannunka a kansa. 19Ka sa shi yă tsaya a gaban Ele'azara firist da dukan jama'a, ka kuma naɗa shi a gaban idanunsu. 20Ka ba shi sashen ikonka, domin dukan jama'ar Isra'ilawa su yi masa biyayya. 21Zai tsaya a gaban Ele'azara firist, wanda zai nemi masa hukuncin Urim a gaban Ubanmu. Bisa ga kalmar Ele'azara za su fita, bisa ga kalmarsa kuma za su shiga—shi, da dukan Isra'ilawa tare da shi, da dukan jama'a.”
22Musa ya yi biyayya ga umarnin Ubanmu; ya ɗauki Yoshuwa ya sa shi yă tsaya a gaban Ele'azara firist da dukan jama'a. 23Ya ɗora hannuwansa a kansa ya naɗa shi, yadda Ubanmu ya faɗa ta wurin Musa.