Shugabannin da Suke Cinye Mutanensu
Zargin yana da hoton cin naman mutum: shugabannin da suke feɗe fatar jama'arsu suna yanyanka su don tukunya. Annabawa suna wa'azin salama ga duk wanda ya ciyar da su; Ubanmu ba zai amsa ba. Saboda waɗannan mutane, za a nome Sihiyona kamar gona, a kuma bar dutsen haikalin ya zama kurmi.
3 1Sai na ce, Ku saurara, ya ku shugabannin Yakubu, da masu mulkin gidan Isra'ila! Ashe, ba aikinku ne ku san adalci ba? 2Ku da kuke ƙin nagarta kuna kuma ƙaunar mugunta, ku da kuke ɓanɓare fatar mutanena da namansu daga ƙasusuwansu; 3ku da kuke cin naman mutanena, kuna ɓanɓare fatarsu, kuna kuma farfasa ƙasusuwansu kucu-kucu; kuna yayyanka su kamar nama don tukunya, kamar tsoka a cikin babbar tukunya. 4Sa'an nan za su yi kuka ga Ubanmu, amma ba zai amsa musu ba; zai ɓoye fuskarsa daga gare su a wannan lokaci, saboda muguntar da suka yi.
5Ga abin da Ubanmu ya ce game da annabawan da suke ɓatar da mutanena. Sa'ad da aka ciyar da su, sukan yi shela, “Salama,” amma su yi shelar yaƙi a kan duk wanda bai sa musu kome a baki ba. 6Saboda haka dare zai sauko muku, babu wahayi; duhu gare ku, babu duba. Rana za ta faɗi a kan annabawa, yini kuma zai yi duhu a kansu. 7Masu gani za su sha kunya masu duba kuma za su ji kunya; dukansu za su rufe bakunansu domin kunya, gama babu amsa daga wurin Ubanmu.
8Amma ni dai, an cika ni da iko—da Ruhun Ubanmu—da kuma adalci da ƙarfi, domin in shelanta wa Yakubu laifinsa da kuma wa Isra'ila zunubinsa. 9Ku saurari wannan, ya ku shugabannin gidan Yakubu da masu mulkin gidan Isra'ila, ku da kuke rena adalci kuna kuma karkatar da duk abin da yake daidai, 10ku da kuke gina Sihiyona da zub da jini Urushalima kuma da mugun aiki. 11Shugabanninta suna yin shari'a don cin hanci, firistocinta suna koyarwa don neman kuɗi, annabawanta kuma suna duba don azurfa; duk da haka suna jingina ga Ubanmu suna cewa, “Ashe, Ubanmu ba ya tare da mu ba ne? Babu masifar da za ta same mu.” 12Saboda haka saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima za ta zama tarin kango, dutsen haikali kuma zai zama tudun da jeji ya rufe.