Tsarin Ubanmu cikin Hukumar Mulki
An sa ikon mahukunta a ƙarƙashin Ubanmu, don haka ana biyan haraji da girmamawa, ba da ɓacin rai ba. Sa'an nan bashi ɗaya kaɗai da ya rage a buɗe shi ne ƙauna, wadda bisa ga ma'anarta ba ta cutar da maƙwabci, ta haka kuma take cika umarnai. Lokaci ya kure; ku yi ado domin hasken rana.
13 1Dole kowa yă yi biyayya ga hukumomin mulki, gama babu wata hukuma sai daga Ubanmu, kuma waɗanda suke nan, Ubanmu ne ya kafa su. 2Saboda haka duk wanda ya yi gāba da hukuma, yana gāba da abin da Ubanmu ya kafa ke nan, kuma masu gāba suna jawo wa kansu hukunci. 3Masu mulki ba barazana ba ne ga ayyuka masu kyau, sai dai ga munana. Kana so kada ka ji tsoron hukuma? Ka aikata nagarta, za ka kuwa sami amincewarta. 4Shi bawan Ubanmu ne, domin alherinka. Amma in ka yi laifi, ka ji tsoro—ba a banza yake riƙe da takobi ba. Shi bawan Ubanmu ne, mai ramuwa wanda yake kawo fushi a kan mai aikata mugunta. 5Saboda haka dole ku yi biyayya, ba domin ku guji hukunci kaɗai ba, har ma saboda lamiri. 6Shi ya sa kuke biyan haraji kuma, gama masu mulki ma'aikatan Ubanmu ne, waɗanda suka maida hankali ga wannan abu. 7Ku biya kowane abin da ake binku: haraji ga mai karɓar haraji, kuɗin fito ga mai karɓar fito, girmamawa ga mai cancantar girmamawa, daraja ga mai cancantar daraja.
Ƙauna Takan Cika Shari'a
8Kada ku ci bashin kowa, sai dai bashin ƙaunar juna, gama wanda yake ƙaunar wani ya cika shari'a ke nan.
9Gama dokokin nan—“Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi”—da kowace doka ta dabam, an taƙaita su cikin magana ɗaya, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
10Ƙauna ba ta yin laifi ga maƙwabci; saboda haka ƙauna ita ce cikar shari'a.
11Ku yi haka, kuna sane da lokacin, lokaci ya yi da za ku farka daga barci—ceto ya yi kusa yanzu fiye da sa'ad da muka fara gaskatawa. 12Dare ya kusa ƙarewa, gari ya kusa wayewa. Saboda haka bari mu tuɓe ayyukan duhu, mu sanya kayan yaƙin haske. 13Bari mu yi zaman kirki, kamar da rana tsaka, ba cikin annashuwar banza da buguwa ba, ba cikin fasikanci da lalata ba, ba cikin faɗa da kishi ba. 14Sai dai ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu; kada ku yi wani shiri na biyan sha'awoyin halin zunubi.