Uba Ya Jagoranci Isra'ila Su Ƙetare Urdun
Kogin Urdun ya cika ya batse, jama'a kuma ba su taɓa bin wannan hanya ba. Ubanmu ya ce wa firistoci su shiga ruwan ɗauke da akwatin, sai da ƙafafunsu suka taɓa shi kafin kogin ya tattaru wuri ɗaya. Dukan al'ummar ta haye a kan busasshiyar ƙasa.
3 1Yoshuwa ya tashi da sassafe, shi da dukan Isra'ila kuwa suka kama hanya daga Shittim, suka isa Urdun, suka kuma sauka a can kafin su ƙetare. 2Bayan kwana uku sai shugabannin suka ratsa sansanin, 3suka umarci mutane suka ce, “Sa'ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubanku wanda firistoci Lawiyawa suke ɗauka, ku bar wurinku ku bi shi. 4Sai dai ku bar nisa tsakaninku da shi, wajen ƙafa dubu uku a awo; kada ku kusace shi, domin ku san hanyar da za ku bi, tun da ba ku taɓa bin wannan hanya ba dā.”
5Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubanmu zai yi ayyukan banmamaki a cikinku.” 6Sa'an nan Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku ƙetare a gaban mutane.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka tafi a gaban mutane.
7Ubanmu ya ce wa Yoshuwa, “Yau zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ila, domin su san cewa yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai. 8Ka umarci firistoci masu ɗaukar akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka kai gaɓar ruwan Urdun, ku tsaya cik a cikin Urdun.’”
9Yoshuwa ya ce wa Isra'ilawa, “Ku zo nan ku saurari maganar Ubanku.” 10Yoshuwa ya ce, “Ga yadda za ku san cewa Uba mai rai yana tare da ku, lalle zai kori Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku. 11Ga shi, akwatin alkawari na Mai Mulkin dukan duniya zai ƙetare a gabanku ya shiga Urdun. 12To yanzu, ku zaɓi mutane goma sha biyu daga cikin kabilan Isra'ila, mutum ɗaya daga kowace kabila. 13Sa'ad da tafin ƙafafun firistoci masu ɗaukar akwatin Uba Mai Mulkin dukan duniya suka sauka a cikin ruwan Urdun, sai ruwan Urdun zai tsinke—ruwan da yake gangarowa daga sama—ya tsaya tsibi ɗaya.”
14Sa'ad da mutane suka bar tentunansu domin su ƙetare Urdun, firistoci suna ɗauke da akwatin alkawari a gabansu, 15sa'ad da masu ɗaukar akwatin suka kai Urdun, ƙafafun firistoci masu ɗaukar akwatin kuwa suka shiga gaɓar ruwa (gama Urdun yakan cika yă mamaye dukan gaɓoyinsa a dukan kwanakin girbi), 16sai ruwan da yake gangarowa daga sama ya tsaya, ya tashi tsibi ɗaya can nesa a Adam, birnin da yake kusa da Zaretan, ruwan kuwa da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Matacce, ya tsinke sarai. Sai mutane suka ƙetare ɗaura da Yeriko. a a v16 Adam gari ne a Kogin Urdun, ba mutumin nan na Littafi Mai Tsarki ba. A Ibraniyanci, Tekun Gishiri. 17Firistoci masu ɗaukar akwatin alkawari na Ubanmu suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun, dukan Isra'ila kuwa suka ƙetare a kan busasshiyar ƙasa, har sai da dukan al'umma suka gama ƙetaren Urdun.