Sabuwar Waƙa
Zabura.
Waƙar nasara ce don abin da aka riga aka gama — ceton da Ubanmu ya samu da ikon hannunsa, ya kuma nuna a fili ga al'umman da suke kallo, yana cika amincinsa ga Isra'ila. Sai kayan kiɗa suka fara, koguna suka tafa, tuddai suka rera waƙa, domin yana zuwa ya yi shari'a da adalci.
98 1Ku rera wa Ubanmu sabuwar waƙa, gama ya yi abubuwa masu ban mamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun kawo masa ceto. 2Ubanmu ya sanar da cetonsa; ya bayyana adalcinsa a gaban al'ummai. 3Ya tuna da madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga gidan Isra'ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Ubanmu.
4Ku yi sowa ta murna ga Ubanmu, dukan duniya; ku ɓarke da waƙar farin ciki, ku kuma yi yabo. 5Ku yi wa Ubanmu yabo da molo, da molo da karar kiɗa. 6Da kakaki da karar ƙaho, ku yi sowa ta murna a gaban Sarki, Ubanmu.
7Bari teku ya yi ruri, da dukan abin da ke cikinsa; duniya da dukan masu zama a cikinta. 8Bari koguna su tafa hannuwa; bari tuddai su rera waƙa don murna gaba ɗaya, 9a gaban Ubanmu, gama yana zuwa yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci, zai kuma hukunta al'ummai da daidaito.