Kafe cikin Uba
Waƙar hawan zuwa Urushalima.
An kwatanta dogara ta fuskar ƙasa. Waɗanda suke dogara ba sa jijjiguwa kamar Dutsen Sihiyona, Ubanmu kuma yana kewaye da su kamar yadda tuddai suka kewaye Urushalima. Mulkin mugaye ba zai dawwama a kan wannan ƙasa ba, domin zai jarabci mutanen kirki su aikata mugunta.
125 1Waɗanda suke dogara ga Ubanmu suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa, amma yana dawwama har abada. 2Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima, haka Ubanmu yake kewaye da mutanensa, yanzu da har abada. 3Sandar mugunta ba za ta zauna a kan ƙasar da aka ba masu adalci ba, domin kada masu adalci su miƙa hannuwansu ga aikata mugunta. 4Ka yi alheri, ya Uba, ga masu kirki, ga waɗanda suke da adalci a zukatansu. 5Amma waɗanda suke karkacewa zuwa karkatattun hanyoyinsu, Ubanmu zai kai su tare da masu aikata mugunta. Salama tă tabbata a kan Isra'ila!