Shugabannin Dangi Sun Yi Magana
Shugabannin iyalan Manassa sun nuna cewa idan 'ya'yan Zelofehad mata suka auri waɗanda ba na kabilarsu ba, za su tafi da ƙasarsu. Hukuncin: suna iya auren duk wanda suka ga ya fi dacewa, amma a cikin iyalin mahaifinsu, don kada gādon wata kabila ya kwarara zuwa wata a ɓoye.
36 1Sai shugabannin iyalan dangin Gileyad, waɗanda suke zuriyar Makir ɗan Manassa, daga dangin Yusufu, suka zo suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, wato shugabannin iyalan Isra'ilawa. 2Suka ce, “Ubanmu ya umarci ranka yă daɗe yă ba da ƙasar gādo ga jama'ar Isra'ila ta hanyar ƙuri'a, Ubanmu kuma ya umarci ranka yă daɗe yă ba da gādon ɗan'uwanmu Zelofehad ga 'ya'yansa mata. 3Idan suka auri maza daga waɗansu kabilan Isra'ila, to, za a ɗauke gādonsu daga gādon kakanninmu a kuma haɗa shi da na sabuwar kabilarsu, ta haka gādon da aka ba mu zai ragu. 4Sa'ad da shekarar Yubili ta Isra'ila ta zo, to, gādonsu zai haɗu da gādon kabilar da suka auru a cikinta, a ɗauke shi daga gādon kabilar kakanninmu.”
5Sai Musa ya umarci Isra'ilawa bisa ga maganar Ubanmu, ya ce, “Abin da kabilar Yusufu suke faɗa daidai ne.
6Ga abin da Ubanmu ya umarta game da 'ya'yan Zelofehad mata, za su iya auren duk wanda suka ga ya fi musu kyau, sai dai cikin dangin kabilar mahaifinsu.
7Kada gādon kowane mutumin Isra'ila yă ƙaura daga kabila zuwa wata kabila, gama kowane mutumin Isra'ila dole yă riƙe gādon kabilar kakanninsa. 8Kowace 'ya mace da ta gāji gādo a cikin wata kabilar Isra'ila, dole tă auri mutum daga dangin kabilar mahaifinta, domin kowane mutumin Isra'ila yă riƙe gādon kakanninsa. 9Kada gādo yă ƙaura daga kabila ɗaya zuwa wata, gama kowace kabilar Isra'ila dole tă riƙe gādonta.”
10Kamar yadda Ubanmu ya umarci Musa, haka 'ya'yan Zelofehad mata suka yi. 11Mala, Tirza, Hogla, Milka, da Nowa, 'ya'yan Zelofehad mata, suka auri 'ya'yan 'yan'uwan mahaifinsu maza. 12Suka yi aure a cikin dangin zuriyar Manassa ɗan Yusufu, gādonsu kuma ya kasance a cikin dangin kabilar mahaifinsu.
13Waɗannan su ne umarnai da ƙa'idodin da Ubanmu ya umarta ta wurin Musa ga jama'ar Isra'ila a filayen Mowab, kusa da Urdun ɗaura da Yeriko.