Isra'ila a Shittim
A Shittim Isra'ila suka haɗa kansu da Ba'al na Feyor ta wurin matan Mowab, fushin Ubanmu kuma ya yi ƙuna cikin annoba. Finehas ya ɗauki mataki da māshi alhali kowa yana kuka, annobar ta tsaya a dubu ashirin da huɗu, aka kuma ba shi alkawarin firistanci na har abada.
25 1Sa'ad da Isra'ila yake zaune a Shittim, sai mutane suka fara yin fasikanci da 'ya'yan Mowab mata. 2Suka gayyaci mutane zuwa hadayun allolinsu; mutane kuwa suka ci, suka kuma rusuna wa allolinsu. 3Saboda haka Isra'ila ya haɗa kansa da Ba'al na Feyor, sai fushin Ubanmu ya ƙuna a kan Isra'ila.
4Ubanmu ya ce wa Musa, “Ka ɗauki dukan shugabannin mutane, ka kuma kashe su a gabana da hasken rana, domin zafin fushina yă juya daga Isra'ila.”
5Musa ya ce wa alƙalan Isra'ila, “Kowannenku yă kashe mutanensa waɗanda suka haɗa kai da Ba'al na Feyor.”
6Sai wani mutumin Isra'ila ya kawo wata mace Bamidiyane wajen 'yan'uwansa a gaban Musa da dukan taron Isra'ila, suna kuka a ƙofar Tentin Sujada. 7Da Finehas ɗan Eli'azar, ɗan Haruna firist, ya ga haka, sai ya tashi daga taron, ya ɗauki māshi a hannunsa. 8Ya bi mutumin Isra'ila cikin ɗakin, ya soke su biyu—mutumin Isra'ila da matar, ta cikinta. Sai annobar da take kan Isra'ilawa ta tsaya. 9Waɗanda suka mutu a annobar kuwa sun kai 24,000.
10Sai Ubanmu ya ce wa Musa,
11“Finehas ɗan Eli'azar, ɗan Haruna firist, ya juyar da fushina daga Isra'ilawa, domin ya yi kishi da kishina a cikinsu, saboda haka ban hallaka Isra'ilawa cikin kishina ba. 12Saboda haka ka faɗa cewa ina ba shi alkawarina na salama. 13Shi da zuriyarsa a bayansa za su kasance da alkawarin firistanci na dawwama, domin ya yi himma dominna, ya kuma yi kafara domin Isra'ilawa.” a a v13 Alkawarin Finehas na firistanci na har abada da kuma aikinsa na kafara suna nuni gaba ga Yesu, firist madawwami wanda kishinsa domin Ubanmu da hadayarsa ta sau ɗaya tak suka kawo salama mai dawwama wadda babu wani firist ɗan adam da zai iya samarwa.
14Sunan mutumin Isra'ila da aka kashe tare da matar Bamidiyane shi ne Zimri ɗan Salu, shugaban wani dangi na kabilar Saminu. 15Sunan matar Bamidiyane da aka kashe kuwa Kozbi ce, 'yar Zur, wanda yake shugaban wani dangi a Midiyan.
16Sai Ubanmu ya ce wa Musa,
17“Ka ɗauki Midiyanawa a matsayin abokan gāba, ka kuma karkashe su, 18gama su abokan gābanku ne ta wurin makircinsu, wanda suka yi muku a kan al'amarin Feyor, da kuma a kan Kozbi 'yar shugaban Midiyan, 'yar'uwarsu, wadda aka kashe a ranar annobar da ta zo saboda Feyor.”