Ubanmu Ya Kawar da Mugun Mulkin Ahaziya
Ahaziya ya yi mulki shekara ɗaya, mahaifiyarsa Ataliya tana ba shi shawara ya aikata mugunta, ya kuma mutu a kisan da Yehu ya yi. Sai Ataliya ta kashe dukan zuriyar sarauta, sai dai jariri ɗaya da matar firist ta ɓoye a gidan Ubanmu har shekara shida, ita kuwa tana mulki.
22 1Mutanen Urushalima suka naɗa ɗansa autan, Ahaziya, sarki a maimakonsa, domin mahara da suka zo tare da Larabawa cikin sansani sun kashe dukan 'ya'yansa maza manya. Saboda haka Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya zama sarki. 2Ahaziya ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyu, ya kuma yi mulki shekara ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri. 3Shi ma ya bi hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ba shi shawara yă aikata mugunta. 4Ya aikata mugunta a gaban Ubanmu, kamar gidan Ahab, gama bayan mutuwar mahaifinsa su ne mashawartansa, har suka kai shi ga hallaka. 5Ya kuma bi shawararsu, ya haɗa kai da Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot-gileyad, inda Arameyawa suka ji wa Yoram ciwo. 6Saboda haka ya koma Yezreyel domin yă warke daga raunukan da ya ji a Rama sa'ad da yake yaƙi da Hazayel sarkin Aram. Ahaziya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezreyel domin yă ga Yoram ɗan Ahab, saboda ya ji ciwo.
7Faɗuwar Ahaziya ta zo daga wurin Ubanmu sa'ad da ya ziyarci Yoram. Da isowarsa, sai ya fita tare da Yehoram don su yaƙi Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubanmu ya shafe domin yă hallaka gidan Ahab. 8Sa'ad da Yehu yake zartar da hukunci a kan gidan Ahab, sai ya sami shugabannin Yahuda da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su. 9Ya kuma nemi Ahaziya, aka kama shi yana ɓoye a Samariya. Suka kawo shi wurin Yehu suka kashe shi, sa'an nan suka binne shi, suna cewa, “Shi ɗan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubanmu da dukan zuciyarsa.” Saboda haka gidan Ahaziya bai sami wani mai ƙarfin da zai riƙe mulki ba.
Yaron da Aka Ɓoye a Gidan Ubanmu
10Sa'ad da Ataliya, mahaifiyar Ahaziya, ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi tsaye domin ta hallaka dukan zuriyar sarauta ta gidan Yahuda. 11Amma Yehoshabeyat 'yar sarki ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda za a kashe, ta kuma ɓoye shi tare da mai renonsa a cikin ɗakin kwana. Ta haka Yehoshabeyat, 'yar Sarki Yehoram, matar Yehoyada firist, 'yar'uwar Ahaziya kuma, ta ɓoye shi daga Ataliya, saboda haka ba ta kashe shi ba. 12Ya kuma kasance a ɓoye tare da su a gidan Ubanmu shekara shida, yayinda Ataliya take mulki a kan ƙasar.