Ubanmu Ya Dakatar da Yaƙin Rehobowam
Rehobowam ya tara sojoji domin ya ƙwato arewa, amma maganar Ubanmu ta tsayar da shi: wannan daga wurina ne, ku koma gida. Maimakon haka ya gina garuruwan Yahuza da garu, firistoci da Lawiyawa waɗanda wuraren sujada na maruƙan Yerobowam suka kore su kuwa suka komo wurinsa, suka ƙarfafa mulkin shekara uku.
11 1Da Rehobowam ya zo Urushalima, sai ya tara gidan Yahuda da Benyamin — zaɓaɓɓun jarumawa dubu ɗari da tamanin — domin su yaƙi Isra'ila su kuma mai da mulki ga Rehobowam. 2Amma maganar Ubanmu ta zo wa Shemaya, mutumin Ubanmu, cewa,
3“Ka gaya wa Rehobowam ɗan Sulemanu, sarkin Yahuda, da kuma dukan Isra'ila da suke cikin Yahuda da Benyamin, 4Ga abin da Ubanmu ya ce, kada ku haura ko ku yaƙi 'yan'uwanku. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan abu daga wurina ne ya zo.” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubanmu, suka juya baya daga kai wa Yerobowam hari.
Rehobowam Ya Ƙarfafa Yahuda
5Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuma gina birane don kāriya a cikin Yahuda. 6Ya gina Baitalami, da Etam, da Tekowa, 7da Bet-zur, da Soko, da Adullam, 8da Gat, da Maresha, da Zif, 9da Adorayim, da Lakish, da Azeka, 10da Zora, da Aiyalon, da Hebron, waɗannan birane masu katanga ne da suke cikin Yahuda da Benyamin. 11Ya ƙarfafa kagarun, ya sa shugabanni a cikinsu, tare da tanadin abinci, da mai, da ruwan inabi. 12A cikin kowane birni ya ajiye garkuwoyi da māsu, ya ƙarfafa su ƙwarai. Ta haka Yahuda da Benyamin suka ci gaba da zama nasa.
13Firistoci da Lawiyawa da suke ko'ina a cikin dukan Isra'ila suka zo wurinsa daga dukan yankinsu, 14gama Lawiyawa suka bar wuraren kiwonsu da dukiyarsu, suka tafi Yahuda da Urushalima, domin Yerobowam da 'ya'yansa sun kore su daga yin hidima a matsayin firistocin Ubanmu. 15Ya naɗa wa kansa firistoci saboda masujadan kan tuddai, da saboda gumakan bunsurai, da saboda gumakan 'yan maruƙa da ya yi. 16Daga cikin kowace kabilar Isra'ila, waɗanda suka kafa zuciyarsu ga neman Ubanmu, Allah na Isra'ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubanmu, Allah na kakanninsu. 17Suka ƙarfafa mulkin Yahuda, suka taimaki Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku, gama sun yi tafiya a hanyar Dawuda da Sulemanu shekara uku.
Iyalin Rehobowam
18Rehobowam ya auri Mahalat, 'yar Yerimot ɗan Dawuda da kuma 'yar Abihayil 'yar Eliyab ɗan Yesse. 19Ta haifa masa 'ya'ya maza, Yewush, da Shemariya, da Zaham. 20Bayanta, ya auri Ma'aka 'yar Absalom, wadda ta haifa masa Abija, da Attai, da Ziza, da Shelomit. 21Rehobowam ya ƙaunaci Ma'aka 'yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwaraƙwaransa, domin yana da mata goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin, da 'ya'ya maza ashirin da takwas, da 'ya'ya mata sittin. 22Rehobowam ya naɗa Abija, ɗan Ma'aka, babban shugaba a cikin 'yan'uwansa, da nufin yă naɗa shi sarki. 23Ya yi aiki da hikima, ya watsa waɗansu daga cikin 'ya'yansa ko'ina a cikin kowane yanki na Yahuda da Benyamin, zuwa kowane birni mai katanga, yana ba su tanadi a yalwace, yana kuma nema musu mata masu yawa.