Kabilun Benyamin: Zuriyar Shawulu
Kabilun Biliyaminu dalla-dalla, an bi su zuwa Gibeyon da Urushalima, har zuwa Kish, Shawulu, Yonatan, da 'ya'yansu da jikokinsu. Sarkin farko na Isra'ila ba shi da labari a nan, sai asalinsa da zuriyarsa kawai, an lissafa shi kamar kowa.
8 1Benyamin ya haifi Bela ɗan farinsa, Ashbel na biyu, Ahara na uku, 2Noha na huɗu, Rafa kuma na biyar. 3Bela yana da 'ya'ya maza. Su ne, Addar, Gera, Abihud, 4Abishuwa, Na'aman, Ahowa, 5Gera, Shefufan, da Huram. 6Waɗannan su ne 'ya'yan Ehud maza, shugabannin iyalai na mazaunan Geba, waɗanda aka kai zaman bauta zuwa Manahat. 7Na'aman, Ahiya, da Gera. Gera ne ya kai su bauta, shi kuma ya haifi Uzza da Ahihud.
8Shaharayim ya haifi 'ya'ya a ƙasar Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba'ara. 9Ta wurin matarsa Hodesh ya haifi Yobab, Zibiya, Mesha, Malkam, 10Yewuz, Sakiya, da Mirma. Waɗannan su ne 'ya'yansa maza, shugabannin iyalai. 11Ta wurin Hushim ya haifi Abitub da Elfa'al. 12'Ya'yan Elfa'al maza su ne, Eber, Misham, da Shemed, wanda ya gina Ono da Lod tare da garuruwan da suke kewayenta, 13Beriya da Shema su ne shugabannin iyalai na mazaunan Aiyalon; su ne suka kori mazaunan Gat. 14Ahiyo, Shashak, Yeremot, 15Zebadiya, Arad, Eder, 16Mika'ilu, Ishfa, da Yoha su ne 'ya'yan Beriya maza. 17Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber, 18Ishmerai, Izliya, da Yobab su ne 'ya'yan Elfa'al maza. 19Yakim, Zikri, Zabdi, 20Eliyenai, Zilletai, Eliyel, 21Adaya, Beraya, da Shimrat su ne 'ya'yan Shimeyi maza. 22Ishfan, Eber, Eliyel, 23Abdon, Zikri, Hanan, 24Hananiya, Elam, Antotiya, 25Ifdeya, da Penuwel su ne 'ya'yan Shashak maza. 26Shamsherai, Sehariya, Ataliya, 27Ya'areshiya, Iliya, da Zikri su ne 'ya'yan Yeroham maza. 28Waɗannan su ne shugabannin iyalai da shugabanni, bisa ga tarihin zuriyarsu; sun zauna a Urushalima.
29Mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon, sunan matarsa Ma'aka. 30ɗansa na fari shi ne Abdon, sa'an nan Zur, Kish, Ba'al, Nadab, 31Gedor, Ahiyo, da Zeker. 32Miklot ya haifi Shimeya. Waɗannan ma sun zauna kusa da 'yan'uwansu a Urushalima.
33Ner ya haifi Kish, Kish ya haifi Shawulu, Shawulu kuma ya haifi Yonatan, Malki-shuwa, Abinadab, da Eshba'al. 34Ɗan Yonatan shi ne Merib-ba'al, Merib-ba'al kuma ya haifi Mika. 35'Ya'yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya, da Ahaz. 36Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Alemet, Azmawet, da Zimri, Zimri kuma ya haifi Moza. 37Moza ya haifi Binea; Rafa ɗansa ne, Eleyasa ɗansa, Azel ɗansa. 38Azel yana da 'ya'ya maza shida. Su ne, Azrikam, Bokeru, Isma'ila, Sheariya, Obadiya, Hanan. Dukansu 'ya'yan Azel ne maza. 39'Ya'yan Eshek maza ɗan'uwansa su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush na biyu, da Elifelet na uku. 40'Ya'yan Ulam maza jarumawa ne ƙwarara, ƙwararrun maharba, suna da 'ya'ya maza da jikoki masu yawa, su 150 ne duka. Dukan waɗannan 'ya'yan Benyamin ne maza.