Uba Ya Yi Magana da Musa
Bayan haihuwa uwa takan zama marar tsarki kwana bakwai domin ɗa namiji, kwana goma sha huɗu kuma domin 'ya mace, sa'an nan ta cika tsarkakewa mafi tsawo kafin ta kusaci kowane abu mai tsarki. Takan kawo ɗan rago da tsuntsu, ko tsuntsaye biyu idan ba ta iya samun ɗan rago ba.
12 1Ubanmu ya yi magana da Musa, ya ce,
2“Ka gaya wa Isra'ilawa, Sa'ad da mace ta yi ciki ta haifi ɗa, za ta ƙazantu har kwana bakwai, kamar yadda take ƙazantuwa a lokacin al'adarta. 3A rana ta takwas kuma za a yi wa yaron kaciya. 4Za ta ci gaba da kasancewa cikin jinin tsarkakewarta har kwana talatin da uku. Kada ta taɓa wani abu mai tsarki, ko ta shiga wuri mai tsarki, sai kwanakin tsarkakewarta sun cika. 5In kuwa ta haifi 'ya mace, za ta ƙazantu mako biyu, kamar lokacin al'adarta, sa'an nan ta ci gaba cikin jinin tsarkakewarta har kwana sittin da shida.
6“Sa'ad da kwanakin tsarkakewarta saboda ɗa ko 'ya mace suka cika, sai ta kawo wa firist a ƙofar Tentin Sujada ɗan rago mai shekara ɗaya hadaya ta ƙonawa, da ɗan tattabara ko kurciya hadaya don zunubi. 7Zai miƙa ta a gaban Ubanmu yă kuma yi kafara dominta, ta kuma tsarkaka daga gudan jininta. Wannan ita ce doka game da mace mai haihuwa, ko ɗa ko 'ya mace ta haifa.
8“In kuwa ba ta da ƙarfin saye rago, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu—ɗaya hadaya ta ƙonawa, ɗaya kuma hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara dominta, ta kuma tsarkaka.” a a v8 Sa'ad da iyali ba su da ƙarfin saye rago, Ubanmu ya ba matalauta dama da wannan ƙaramar baiwa — wannan kuma ita ce ainihin hadayar da Maryamu ta kawo sa'ad da ta miƙa Yesu a Haikali.